Skip to main content

Posts

Showing posts from 2023

Me Ku Ka Sani Game Da Labari Maras Daɗi (Negative Story)?

Galibin wasu mutane na ganin 'yan jarida ba su cika bayar da labarai ma su daɗi ba face waɗanda suka shafi tashin hankali da tonon silili da ƙwanƙwanto da kuma na haɗurra. Wannan fahimta kuwa na da nasaba da kasa fahimtar aikin jaridar kansa da wanda ke yin sa. Ni a ganina duk wani labari da ya shafi ayyukan muggan mutane da ya munanawa mutane na gari shi zan mayarwa hankali domin fallasa mai mugunta da farantawa wanda aka zalunta. Bari mu soma da mai sauƙi kafin mu duba ma su sarkakiya. Idan haɗari ya faru, misali na mota ko jirgin sama ko na kasa ko kuma gobara ko ambaliyar ruwa; za mu bayar da labarin. Shin ka san ba muna bayar da labarin ne saboda kawai a ji an mutu ko an kaririye ko an yi hasarar dukiya ba? GA AMSA:  Game da haɗari ko gobara da sauran iftila'i mu kan bayar da wannan labari saboda bayyana halin waɗanda matsalar ta rutsa da su, domin samun agajin hukumomi da masu iya tallafawa. Mu kan bayar da labarin saboda jawo hankalin hukumomin tsaro da saura

Sheƙar Tsuntsu Da Ta fi Kowace Girma A Duniya

A kan samu irin wannan sheƙar tsuntsun a ƙasashe kudancin Afirka irin Botswana da Namibiya. Abin mamaki shi ne wani ɗan ƙaramin tsuntsu ne mai suna Philetairus socius kan yi wannan sheƙa .   Ta yi kama da saƙar zuma, kuma ya kan nemi bishiyoyi masu ƙarfi kamar gawo da bagaruwa da farar ƙaya sannan ya yi wannan sheƙa. Ta kan jure ruwan sama da zafin rana har ma da tsananin sanyin hunturu. A cikin sheƙa ɗaya akan samu ɗakuna kamar ɗari, ƙofofin kusa da juna. Masu nazarin rayuwar tsuntsaye na ganin wannan tsuntsu shi ne irin sa na farko a duniya ɗan ƙarami da kan gina sheƙa mai girma kamar wannan. Faɗin sheƙar ya kan iya kai har ƙafa 20 tsawonta kuma ƙafa 10. 

Barista Yunusa Ari Ya Yi Ɓatan Dabo

Dakataccen kwamishin hukumar zaɓe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaƙalar da ake zargin sa da ita. Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka. Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya ɗaukar kiran waya kuma sun ma daina jin ɗuriyarsa gaba ɗaya. Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta ɗauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buƙatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaƙulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a". Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun gabanin a kammala tat

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Tsaunin Hin Sam Wan Mai Ɗimbin Shekaru A Duniya

Tsaunukan Hin Sam Wan , da kuma aka fi sani da Dutsen Whale Uku, wasu tsaunuka ne ma su ban sha'awa da suka kai kimanin shekaru miliyan 75.  Suna cikin daga tsaunukan ƙasar Thailand masu ban mamaki.  Sunansu ya samo asali ne daga kamanninsa, idan aka dubi tsaunin daga sama daga sama za a ga ya yi kama da dangin whales wato dabbar nan ta tekun mai kama da kifi whale.

Putin Ya Ziyarci Sansanin Soja Na Kherson Da Ke Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ziyarci yankunan Ukraine da aka mamaye a karo na biyu tun bayan ƙaddamar da wani gagarumin farmaki, kamar yadda fada Kremlin ta sanar a yau Talata. Putin ya ziyarci hedkwatar soji a yankin Kherson na kudancin ƙasar Ukraine da kuma hedkwatar tsaron Rasha da ke yankin Luhansk. Tafiyar ta zo ne a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare a gabashin Ukraine. Jaridar ƙasar Rasha ta The Moscow Times   https://www.themoscowtimes.com/2023/04/18/putin-visits-occupied-ukraine-territories-a80862 ta bayyana cewa Fadar Kremlin ba ta bayyana takamaiman lokacin da tafiyar ta gudana ba kuma hotunan ziyarar biyu sun nuna Putin sanye da tufafi daban-daban.

Binani Na Neman Kotu Ta Tabbatar Da Ita Wadda Ta Lashe Zaɓen Adamawa

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a ranar Litinin sun fito kan tituna domin nuna adawa da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa. Sai dai ita Binani ta buƙaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga sauya matakin da aka ɗauka na ayyana ta da a ka yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen.  A wata buƙata da ta shigar a ranar Litinin, mai neman izinin kotun ya nemi izinin kotun ta ba ta damar shigar da buƙatar neman umarnin haramtawa INEC daga ɗaukar duk wani mataki na watsi da sanarwar da aka yi a ranar 16 ga Afrilu da Kwamishinan zaɓen jahar, Barista Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta samu ƙuri'u mafifi rinjaye kuma ta lashe zaɓen alhali ba a kammala tattara sakamakon zaɓen gaba ɗaya ba. Ta kuma nemi a ba da umarnin hana hukumar zabe ta INEC, da wakilinta nadawa ko kuma duk wanda ke wakiltarta daukar wasu matakai na bayyana wanda ya lashe zaben gwamna da ak

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey

Ko Kun San Yadda Gidajen Samudawa Su Ke?

Samudawa su ne mutanen Annabi Saleh (AS) waɗanda ke da girman jiki da tsawo tamkar bishiyar dabino.   Waɗannan wasu daga gidajen Samudawa ne da suka rage a halin yanzu. Ana kiran wajen da suna (Mada’in Salih) ko Al-Hijr da Larabci,  (ٱلْحِجْر‎‎). Yankin na nan a Al-‘Ula cikin lardin Madina a Hejaz, ta ƙasar Saudiyya. A shekarar 2008, Hukumar Kula Da Adana Kayan Tarihi Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana Mada’in Salih  a matsayin wani wajen da take girmamawa, wurin tarihi na Hegra  na nan nisan kilomita 20 arewa da garin Al-‘Ula, tafiyar mil 250 arewa maso yammacin birnin Madina. Samudawa sun wanzu shekaru ɗari bakwai da goma sha biyar kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Mutane daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci wurin, domin ganin ikon Allah.

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Filato

Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Mai Tumbi da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni da aka tura ‘yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da rikincin ya shafa Babban Daraktan Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya a Jihar Filato Joseph Lengmang, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce sun yi matuƙar baƙin ciki da yadda lamarin ya faru, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuwa da dukiya mai ɗimbin yawa.

An Ɗaure Wani Ɗan Jaridar Rasha Kan Sukar Putin

Wata kotu a kasar Rasha ta yankewa ɗan jarida hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa zargin sa da yin kira da a hambarar da gwamnatin shugaba Vladimir Putin bayan mamayar da ya yi ma ƙasar Ukraine a bara. Shafin yanar gizo na ‘yan shafin yanar gizo na jami'an tsaron 'yan sanda na OVD Info   ya ruwaito ranar Juma’a cewa, an kama Kirill Akimov, mai shekaru 52 a watan Yuni, bisa zargin yin kiraye-kirayen da ka iya kai wa ga tashin hankali yayin gabatar da shiri a wani gidan rediyo a ranar 14 ga Maris, 2022.  Akimov, wanda ya fito daga Jamhuriyar Mordovia ta tsakiyar Rasha, mai tazarar kilomita 400 gabas da birnin Moscow. Kotun soji da ke Yekaterinburg a ranar Laraba ta samu Akimov da laifuffuka biyu na ingiza jama'a su yi bore da kuma aikata ta’addanci, a cewar wata kotu.

Binani Ta Zama Mace Ta Farko Da AKa Zaɓa Gwamna A Najeriya

A wani abinda ba saban ba, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jahar Adamawa. Kwamishinan zaɓen jahar Adamawa, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen ana tsakiyar tattara sakamakon zaɓen. An bayyana sakamako daga ƙananan hukumomi 10 cikin 20 yayin da aka dage ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen har zuwa karfe 11 na safe. Sai dai Ari ya sanar da sakamakon ƙarshe awa ɗaya kafin lokacin da aka tsara. Gwamnan jahar Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba kafin a bayyana hakan. Wasu magoya bayan jam’iyyar PDP a zauren sun nuna rashin amincewarsu da dalilin da ya sa kwamishinan zaɓe ya sanar da sakamakon maimakon baturen tattara sakamakon zaɓe a al'adance.

Halin Da Ake Ciki Kan Yunƙurin Juyin Mulki A Sudan

Jami'an Ɗaukin Gaggawa don Tallafa ma Tsaro a Sudan na Rapid Support Forces (RSF) a yau asabar sun ce sun ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa da gidan hafsan hafsoshin soji da babban filin jirgin sauka da tashin jiragen sama a birnin Khartoum a wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a lokacin da rikici ya ɓarke tsananinsu da sojoji. Rundunar ta RSF wacce ta zargi sojojin da fara kai mata hari, ta kuma ce sun ƙwace tashoshin jiragen sama a arewacin garin Merowe da kuma El-Obeid a yammacin ƙasar. Rundunar sojin saman Sudan na ci gaba da fatattakar mayaƙan RSF, a cewar wata sanarwa rundunar.   Wasu gidajen talabijin sun nuna wani jirgin soji a sararin samaniyar birnin Khartoum, amma Tantabara News ba ta tabbatar da sahihancin labarin. Rahotanni da ke shigo muna yanzu haka na bayyana cewa ana iya jin ƙarar harbe-harbe a sassa da dama na birnin Khartoum inda wasu shaidun gani da ido da ke bayar da rahoton harbe-harbe a garuruwan da ke makwabtaka da su, lamarin da ya sa ake fargaba

Iran Ta Sha Alwashin Murƙushe Masu Tallata Manufar Cire Hijabi

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilun da ya gabata ne mataimakin babban lauyan ƙasar Iran ya bayyana cewa, za a gurfanar da mutanen da ke ƙarfafa mata gwiwar cire hijabi a gaban kotunan laifuka, kuma ba za su sami damar daukaka ƙara kan duk wani hukunci da aka yanke musu ba. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar mata da ke bijirewa dokokin sanya hijabi da Iran ta sanya, inda suke bayyana a manyan kantuna da gidajen cin abinci da shaguna da sauran wuraren taruwar jama'a.  A cikin 'yan watannin nan wasu mata masu fafutuka sun fito fili sun yaɗa hotunan kansu a shafukan sada zumunta ba tare da lullubi ba. Jami'an tsaron 'yan sandan Iran a ranar Asabar ɗin makon jiya, sun sanya na'urorin ɗaukar hoto a wuraren taruwar jama'a don tantancewa da kuma hukunta matan da aka gano ba su sanye da hijabi, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Iran suka ruwaito.   Kamfanin dillancin kabaran Reuters ya ruwaito mataimakin babban lauyan gwamnatin ƙa

Wanene Ɗan Jarida?

Ɗan jarida mutum ne kamar kowa, sai dai tunaninsa da manufofinsa kan tafi daidai ne kawai da ra'ayin MASU SAURARO ta fuskokin da suka shafi aikinsa. Ya zama mai wakiltar waɗanda ba su da baki ne ko kafafuwan zuwa, kuma idanuwan talakawa a kowane lokaci. Idan ka nuna ma sa launi shuɗi, ƙoƙarin ya ke ya tabbatar da launin nan shuɗi ne ziryan ko yana da garwaye? Idan ka ce ma sa labarin abu kaza ya faru, ba zai ce a'a ba kuma ba zai ce eh ba, aikinsa shi ne TABBATARWA . Idan mai sauraro namiji ne ko mace ko mai ra'ayin wani addini ko akida ko mai kuɗi ko talaka, ɗan jarida kan GIRMAMA kowa, kuma zai ɗauki kowa a matsayin DAIDAI ta fuskar ba su damar bayyana ra'ayoyinsu. Ɗan jarida kan tafi da zamani, ya kuma rungumi fasahar da ƘIRƘIRA ta kawo domin tafiya daidai lokaci. A kowace marra GASKIYA ita ce madogarar ɗan jarida, kuma wannan kan ƙara sa masu sauraro su amince da shi. Amma kuma, dole ne ɗan jarida ya zama MAI IKON KANSA , ba zai yi ma kowa alfarma b

Dalar Amurka Na Fuskantar Barazanar Durkushewa

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF. Lula ya yi waɗannan kalamai a wata ziyarar aiki da ya kai Chana, jiya Alhamis a birnin Shanghai a wani bikin kaddamar da takwaransa, Dilma Rousseff a matsayin sabuwar shugabar bankin raya kasashen BRICS, da gamayyar kasashenn Brazil da Rasha da Indiya da Chana da kuma Afirka ta Kudu suka samar. "Me ya sa kowace ƙasa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuɗin duniya?"  Ya ƙara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuɗin da zai gudanar da hulɗar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran ƙasashen duniya? Ya ce yana mamakin yadda ƙasashe cike da rauni  su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuɗaɗensu. A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya

Tinubu Na Gaban Tambuwal A Sokoto

Asiwaju Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya ba Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP a jihar Sokoto rata a jahar.   Duk da cewa akwai kananan hukumomi 23 a jihar, Tinubu ya tattara mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi 10. Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 101,608, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 98,080 yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya zo na uku da kuri’u 314 sannan Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 171. Kananan Hukumomin Da Aka Samu Sakamakonsu TURETA  Waɗanda aka yi ma rajita: 40,746  Waɗanda aka tantance: 16,516  APC 7, 684  LP.  1  NNPP.  9  PDP.  8, 144  KWARE  Waɗanda aka yi ma rajita 74,056  Waɗanda aka tantance 24,776  APC 10,485  LP.  63  NNPP.  11  PDP.  12,242  BODINGA  Waɗanda aka yi ma rajita 86,139  Waɗanda aka tantance 28,054  A 1  AA0 ku  AAC.  9  ADC.  21  ADB.  93  APC 13,384  APGA 26  APM.  7  APP 5  BP.  1  LP.  10  NNPP.  39  NRM.  33  PDP.  13,559  PRP  1

Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa Kai Tsaye

Za mu ci gaba da kawo muku sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki na ƙasa. Hoto: BBC Hausa

An Kashe Ɗan Takarar Jam'iyyar Labour A Kudu Maso Gabas

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaɓen 2023. Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, ɗan takarar ɗan majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, sa’o’i 48 kafin gudanar da zaɓen. An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a ƙaramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaƙin neman zaɓe. An kuma ce masu kisan sun kona shi da magoya bayansa bayan sun tare da shi a cikin motarsa. Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, waɗanda ke ganin barazana ce ga bunƙasar jam’iyyar a jihar. Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaɓe.  Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sha alwashin

Tsakanin Kyanwa Da Ɓeraye...

Mage ta zauna ta yi jugum ta rasa abinda ke yi mata daɗi, ko ina sai karɓar saƙon zagi da suka take yi daga dabbobin dawa da suka kiwata ta da guminsu saboda yaƙi da ɓeraye. An zargi Mage da ba wa ɓeraye damar sace daddawar jamhuriya ba tare da ɗaukar mataki ba. Ga shi kuma wa'adin mulkin Mage ya ƙare dole ta koma gefe ta zama ƴar kallo. Shin ko me Mage zata yi don kawo ƙarshen ɓarnar ɓeraye da suka tara daddawar jamhuriya don gadar kujerar Mage? Mage ta fesa fiya-fiya akan wannan daddawar miya, wanda yanzu haka ƙwari da ɓeraye suka gano Mage ta shirya ganin bayan su don haka suka haɗa kai domin yaƙar ta. A baya kowane ɓera mai riƙe da ragamar mulki ya ci karensa ba babbaka. Ya yi mulkin mallaka da kama karya. Ya saci daddawar miya son ransa, ya yaƙi duk wanda ya ɗaga masa murya, ya halatta kansa rusa akurkin kaji ba bisa ƙa'ida ba, ya mallake shingayen ƙananan dabbobi ba bisa ƙa'ida ba. Duk da babbar majalisar dokokin zartaswa ta hana su ba su yarda ba, amma a

DA DUMI DUMI: CBN Ya Ce Kada Bankuna Su Amshi Tsofaffin Kuɗi

'Yan sa'o'i da fitar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sanarwar cewa bankuna na iya amsar tsofaffin takardun kuɗin naira 500 da naira 1000 daga hannun jama'a, to sai dai Bankin na CBN ya yi amai ya lashe in da ya ce bai amince bankuna su amshi takardun kuɗin naira ga kowa ba sai dai mutum ya kai kuɗinsa da kansa kamar yadda aka tsara da farko.

Buhari Ya Amince A Kashe Tsohuwar Naira 200

A wani jawabi da ya yi a yau Alhamis, shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Babban Bankin Najeriya CBN umurnin sake fito da tsohuwar naira 200 a hannun al'umma domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara. Buhari ya bayyana cewa an samu muhimman nasarori ta dalilin canjin fasalin kuɗi da aka yi. Ya nunar da cewa yana sane da irin halin matsin da 'yan Najeriya suka shiga, akan haka suna iya amfani da tsohuwar naira 200 sai dai su kai tsofaffin kuɗaɗe da suka haɗa da naira 500 da kuma naira 1000 a bankin CBN. Menene ra'ayinku kan wannan batu?

CBN Insists On Deadline Despite Court Order

The Central Bank of Nigeria CBN has insisted that its February 10th deadline for the validity of old naira notes still stands. The CBN governor, Godwin Emefiele, made the disclosure while briefing the diplomatic community at the ministry of foreign affairs in Abuja. The development comes despite the ex-parte order of the Supreme Court which restrained the federal government from implementing the February 10th deadline, pending the hearing of the matter on February 15th. Emefiele said the situation is substantially calming down since the commencement of over-the-counter payments to complement ATM disbursements and the use of super-agents. He added that there is no need to consider any shift from the deadline of February 10th.

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak. Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kotu Ta Tabbatar Da Peter Obi Matsayin Ɗan Takarar Jam'iyyar LP

Kotun ɗaukaka ƙara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa. Waɗanda ake ƙarar su ne Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma ɗan takararta Mista Peter Obi. Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alƙalai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji. Alaƙalan kotun sun nemi masu saka ƙarar da su biya waɗanda ake ƙara tarar naira dubu ɗari biyu a dalilin ɓata mu su lokaci.

Tinubu Zai Dawo Da Tsoffin Kuɗi - El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya roƙi jama'a cewa kowa ya yi amfani da tsoffin kuɗi daga nan har shekara huɗu. A cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon minti huɗu da daƙiƙa talatin da bakwai, an ga gwamnan na bayyana cewa ya bayar da umurnin duk wani ɗan jahar da ke kasuwanci kada ya fasa amfani da tsoffin kuɗaɗe. "Duk wani ɗan jahar Kaduna daga nan har shekara huɗu in dai an zaɓi APC, Uba zai mayar masa da kuɗinsa". In ji gwamna El-Rufai. A cewarsa wannan saƙo ne daga ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda kuma in ji gwamnan da an zaɓi Tinubu zai sauya wannan tsarin canjin fasalin kuɗi nan take in da zai dawo da tsoffin da mutane ba su kai banki ba. Saboda haka ya umurci jama'a da kada kowa ya kai kuɗinsa banki. Ya ƙara da cewa da zarar an zaɓe su, ya ɗauki alkawarin amsar kuɗin mutane ya tilasta Babban Bankin Najeriya CBN ya canza su musu da sababbi. Ya ci gaba da cewa, "Ku gaya ma kowane ɗan kasuwa, ya karɓi tsohon

PDP Na Shirin Korar Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da ƙara domin hana wani sabon yunƙurin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki mataki ga duk masu wannan aniya.  Ɗaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan ƙarar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da ƙara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN);  Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.”   Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi. Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP ƙadangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.  

Japan Ƙasar Da Kowa Tsoho

A ƙasar Japan da ke gabashin Asiya, adadin haihuwa a shekara ya ragu zuwa kasa da dubu 800 a karon farko a shekarar 2022. Ya zuwa farkon shekarar 2023, kashi 29 na al'ummar Japan mai mutane miliyan 124.77 na da shekaru 65 ne ko sama da haka, kuma kashi 11.6 na tsakanin shekarun 0 da 14. Japan ita ce ƙasa ta farko a duniya bisa ga jimillar yawan jama'a masu shekaru 65 zuwa sama. Firaministan ƙasar, Kishida Fumio ya sanar da cewa Japan na gab da rasa ayyukanta na zamantakewar al’umma sakamakon raguwar yawan haihuwa kuma a bana za su mai da hankali kan manufofin renon yara. Hukumar Kula da Yara da Iyali, mai alaƙa da gwamnatin ƙasar za ta fara aiki a watan Afrilu. Kisida ya bayyana cewa suna shirin ruɓanya kasafin kuɗin manufofin da suka wajaba daga yanzu zuwa watan Yuni. Duk da ci gaban da ƙasar Japan ke da shi a fannonin ƙere-ƙere da fasaha, rashin wadattatun matasa ya sa tana fuskantar matuƙar barazana ga ƙarewar jama'a.

Jam'iyyu 13 Sun Yi Barazanar Ƙauracewa Zaɓe A Najeriya

Gamayyar jam'iyyun adawa 13 sun bayyana cewa za su ƙauracewa shiga zaɓe muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin amfani da tsofaffin kuɗaɗe daga lokacin da aka ɗiba tun da farko. Shugaban jam'iyyar AA Kennetth Udeze ne ya fitar da wannan sanarwa, in da ya ce canjin fasalin kuɗi da CBN ya fito da shi zai haifar da babban tasiri a tattalin arziki da fannin tsaro kana sun kai matsayar watsi da sabon matakin da gwamnonin APC suka ɗauka da suka haɗa da na Kaduna, Malam Nasiru El-rufai da na Zamfara Bello Mutawalle da na Kogi Yahaya Bello, na maka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu kan sauya takardun kuɗi da ya yi. A Najeriya akwai jerin jam'iyyu 18 da za su fafata a babban zaɓe mai zuwa sai dai 13 daga ciki sun yi barazanar janye jikinsu daga shiga zaɓen muddin aka ƙara lokacin amfani da tsofaffin kuɗaɗe. Menene ra'ayinka kan wannan batu?

Yadda Masu Kuɗi Da Ruwa Suka Cika Harabar ATM

Rahotonni da ke ci gaba da shigo muna yanzu haka, na nuni da cewa ɗaruruwan mutane na ta yi dogayen  layuka a gaban na'urar cirar kuɗi ta ATM da ke bankuna, inda suke amfani da wani salo na biyan mutane domin su ciro mu su kuɗi. Wani da muka zanta da shi mai suna Lawal Mai Masara, ya shaida muna cewa, tun jiya ya ke kan layi, kuma har yanzu bai kai ga samun kuɗin ba saboda masu sana'ar POS da masu kwashe kuɗi su sake adanawa sun cika ko'ina. "Za ka ga mutane riƙe da katunan cirar kuɗi fiye da 10 inda suke tura ma wasu kuɗi su rarraba musu katunan domin a cire mu su kuɗin a ATM daga baya su bayar da naira dubu akan duk dubu goma da aka cire mu su". In ji shi. Mutumin ya ƙara da cewa wannan na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa ƙarancin kuɗi tsakanin mutane a Najeriya.musamman arewa. Wannan sabon matakin ya nuna irin yadda mutane ke jefa kansu a halin tasku ta hanyar ci gaba da kwashe kuɗaɗen da jama'a ya kamata su samu. Wani ganau

Wike Ya Tona Magoya Bayan Atiku A Fadar Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar masa da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da magoya bayansa, na taƙama da cewa ba sa buƙatar goyon bayan gwamnonin G5 kafin su ci nasara zaɓe, saboda wasu tsiraru a fadar shugaban ƙasa sun ba su tabbacin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Jaridar POLITICS NIGERIA  ta ruwaito cewa gwamnan yayi magana ne a garin Ibaka a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas na ƙaramar hukumar Okrika a ranar Juma’a. "Na ce an ba su tabbaci, amma wannan zaɓen ba zai dogara ne akan wannan tabbacin ba, yana kan tabbacin mutane ne,” in ji Wike. Gwamna Wike dai ya dage cewa har yanzu Atiku na buƙatar jihar Ribas don samun nasara ko kuma ya faɗi zaɓe a 2023. A cewarsa, “ko kuna so ko ba ku so, dole ne ku buƙaci jihar Ribas. Idan ba ku buƙatar Jihar Ribas to dole ne ku sha ƙasa. Idan kun ce ba ku son mu, lallai kuwa za ku gaz

Canjin Kuɗi Alfanu Ne - Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuɗi, in da ya ce yana da muhimmanci. Ya roƙi 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa  ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuɗi ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasa  da walwalar jama'a duk da akwai buƙatar a inganta shi. Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ƙarshen makon nan. Peter Obi dai ya taɓa zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaɓe mai zuwa.

INEC Ta Yaba Yadda Na'urar BVAS Ke Aiki

Shugaban Hukumar Zaɓe INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa gwajin da aka yi na tantance masu jefa kuri'a ya nuna na'urar BVAS da aka fito da ita na yin aiki yadda ya dace. Shugaban hukumar ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Tarayya Abuja. Ya ce "naurar na iya tantance masu zaɓe cikin dakika 30 kuma babu wata alamar tasgaro a tattare da ita". Farfesa Yakubu ya ce sun tanadi na'urorin wucin gadi ko da aka yi wasu daga cikin na'urorin su kasa lokacin da ake tantance mazu jefa kuri'a da su.