Skip to main content

Posts

Showing posts from August 12, 2022

'Yan Jarida Na Shan Ɗauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci ɗaurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da ƙasarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar ƙasa, sakamakon ɗaga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai ɗauke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaƙi”. Gwamnatin Rasha ta daɗe tana ɗaure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaƙin  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waɗanda aka samu da laifin watsa labarun ƙarya  tsawon shekara goma a gidan jarum.

Cire Iyorchia Ayu Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Kasada Ce – Debo Ologunagba

A wani zaman sulhu da ake ci gaba da yi a Abuja, gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da tsohon mataimakain jam’iyar PDP na yankin kudu, Chif Olabode George, na cikin sahun gaba wajen ganin jam’iyar ta cire shugabanta na yanzu, Iyochia Ayu daga muƙaminsa muddin a na neman zaman sulhun ya kai ga haifar da ɗa mai ido. A cewar su, hakan ne kawai zai iya samar da daidaito ga yankin kudancin Najeriya kasancewar ba adalci ne ba ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iya su fito a yanki guda ba. To, amma kuma wannan buƙata ta gamu da cikas in da a yayin hirarsa da manema labarai a Abuja, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ba za ta saɓu ba, domin cire shi kasada ce, da za ta iya jefa PDP cikin sabon ruɗani.  Ya ƙara da cewa, “ai a fili take ƙarara, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar duk lokacin da aka cire shugaban jam’iyya a bisa kowane dalili ne kuwa, to mataimakinsa kan maye gurbinsa kuma ya zama sun fito daga shiya ɗaya. Kazalika, kundin tsarin mulki