Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da Æ™ona gidaje a rikicin da ya É“arke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Mai Tumbi da ke Æ™aramar hukumar Mangu a jihar Filato. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni da aka tura ‘yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da rikincin ya shafa Babban Daraktan Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya a Jihar Filato Joseph Lengmang, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce sun yi matuÆ™ar baÆ™in ciki da yadda lamarin ya faru, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuwa da dukiya mai É—imbin yawa.