Skip to main content

Posts

Showing posts from January 13, 2021

Da Dumi Dumi - An Tsige Shugaba Trump

Majalisar wakilan Amurka sun samu yawan kuri'un da za su kai ga tsige shugaba Donald Trump. Wannan ya tabbatar da shi a matsayin shugaban Amurka na farko da ka tsige har sau biyu. Kuma wannan zai hana ma sa sake rike kowane irin mukamin siyasar kasar nan gaba da kuma bada damar gurfanar da shi don fuskantar tuhuma a gaban kotu. Ga jerin shuwagabannin Amurka da aka taba tsigewa:  A shekarar 1868 an tsige shugaban Amurka Andrew Johnson,  Sai kuma shugaba Bill Clinton da aka taba tsigewa a 1998. Bayan sa kuma sai shugaban Amurka mai barin gado Donald J. Trump shi kuma  a 2019. Bayan nan kuma yau 13 ga watan Janairun 2021 an sake tsige tsohon shugaban a karo na biyu.

An Soma Jefa Kuri'ar Tsige Trump

'Yan majalisar wakilan Amurka yanzu haka sun soma jefa kuri'ar tsige shugaba Donald J. Trump. Sun soma kada kuri'ar ne bayan kammala muhawarar da ta bada damar ci gaba da daukar mataki na gaba, wanda shi ne kada kuri'ar amincewa ko akasin haka. An dai baza dubban jami'an tsaron soji a ko'ina ciki da harabar majalisar dokoki ta Capitol Hill don shirin ko ta kwana. Bayan kammala jefa kuri'ar daga baya za a turawa majalisar dattijai don daukan mataki na gaba da zai iya kai ga tsige shi ko sabanin haka. Idan har haka ta tabbata zai zama kenan Trump shi ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige har sau biyu. Wannan sabon matakin na da nasaba da jawaban shugaban a makon jiya, da 'yan majalisar suka ce sun kai ga tunzura magoya bayansa har suka kai wa majalisar hari da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, ciki kuwa har da jami'in dan sanda da ke kare masu zanga-zangar daga kutsa kai ginin majalisar.

Matsalar Tsaro Ta Addabi Jahar Sokoto

A daren jiya Talata ne wasu yan bindiga sukayi dirar mikiya a wani kauye mai suna Chacho da ke karamar hukumar mulki ta Wurno da ke jahar Sokoto. Rahotanni na cewa maharan sun kai wa wani Dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu samame ne da niyyar hallaka shi, amma da hakansu ba ta cimma ruwa ba suka yi awon gaba da mahaifinsa hadi da matarsa da kuma harbin kanensa, tare da karbar kudin da suke mallakarsa ne kimanin naira dubu dari shida da sittin. Maharan sun kuma harbe wani dan banga har lahira, mai suna Malam Rabi'u. Wannan lamarin yawitar hare-hare a jahar Sokoto na neman gagarar kundila, domin kwana daya kawai kafin wannan harin wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani gari da ke karamar hukumar ta Wurno da suka karbi kudi naira miliyan daya daga hannun wani dan kasuwa kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar kama biyar daga cikin su.