Skip to main content

Posts

Showing posts from March 26, 2022

An Zabi Abdullahi Adamu Shugaban Jam'iyyar APC

Getty images Jam'iyyar APC ta cimma matsayar zabar tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, a matsayin sabon shugabanta. Kimanin 'yan takara shida ne suka janye daga neman mukamin, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura da tsohon gwamnan jahar Borno Ali Modou Sheriff da tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar Mafara da sauran su. Tun da farko dai an bayyana Abdullahi Adamu a matsayin dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke marawa baya.

Sabon Rikici: Bangaren Abdul'aziz Yari Ya Aike Ma Buhari Sako Mai Zafi

A wani abinda ake ganin bai rasa nasaba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nace akan samar da maslaha a zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa maimakon gudanar da zabe, ya sa bangaren Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jahar Zamfara ya fito fili yana Allah wa dai da matakin shugaban kasa. Yanzu haka jam'iyyar APC na ci gaba da gudanar da babban taronta na kasa a Abuja. Ku latsa hoton da ke kasa don sauraren kalaman bangaren na masu goyon bayan Yari: