Getty images
Jam'iyyar APC ta cimma matsayar zabar tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, a matsayin sabon shugabanta.
Kimanin 'yan takara shida ne suka janye daga neman mukamin, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura da tsohon gwamnan jahar Borno Ali Modou Sheriff da tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar Mafara da sauran su.
Tun da farko dai an bayyana Abdullahi Adamu a matsayin dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke marawa baya.
Comments