Skip to main content

Posts

Showing posts from February 23, 2023

An Kashe ʊan Takarar Jam'iyyar Labour A Kudu Maso Gabas

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaɓen 2023. Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, ɗan takarar ɗan majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, saā€™oā€™i 48 kafin gudanar da zaɓen. An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a ʙaramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaʙin neman zaɓe. An kuma ce masu kisan sun kona shi da magoya bayansa bayan sun tare da shi a cikin motarsa. ʊan takarar gwamna na jamā€™iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jamā€™iyyun siyasa na yi wa ā€˜yaā€™yan jamā€™iyyarsa kisan gilla, waɗanda ke ganin barazana ce ga bunʙasar jamā€™iyyar a jihar. Peter Obi, ɗan takarar shugaban ʙasa na jamā€™iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaɓe.  Wasu da ake zargin ā€˜yan bindiga ne sun sha alwa...