Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2026

Turai na fuskantar tsananin zafi

Burtaniya  Wani matsanancin yanayin zafi ya karaɗe yammaci da arewacin Turai, inda yanayin zafi ya zarta yadda aka saba sosai, kuma ya kai yanayin da aka jima ba a gani irinsa ba a ƙasasahe da dama. Birtaniya da Faransa sun fuskanci yanayin zafin da ba su taɓa ganin irinsa ba a watan Mayu, yayin da iska mai huci ta sa zafin ya kai ƙoluwar da ba a saba ganin irinsa ba ko da a lokacin tsanananin zafi.  Paris a Faransa  Jami’an kula da yanayi sun yi gargaɗin cewa yanayin zafin wata alama ce ta ɗumamar duniya.