Dakataccen kwamishin hukumar zaÉe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaÉan bayan da shugaban Ęasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaĘalar da ake zargin sa da ita. Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka. Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya Éaukar kiran waya kuma sun ma daina jin Éuriyarsa gaba Éaya. Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta Éauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buĘatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaĘulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a". Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaÉen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ęahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaÉen tun gabanin a kammala tat...