Skip to main content

Posts

Showing posts from 2022

President Buhari Opens The Nigerian Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto

President Muhammadu Buhari  declared open the Nigerian Army Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto. The conference tagged: “Building a Professional Nigerian Army for the 21st Century Security Environment” was commenced at the multipurpose Hall of the International Conference Center Kasarawa, in Sokoto State. President Buhari said Nigerian Army has over the years demonstrated its capacity and zeal in defending Nigeria’s territorial integrity and sovereignty against external aggression and giving aid to civil authority in mitigating internal security challenges in the country. He explained that under his administration from 2015 to date, the Nigerian Army has achived a significant success in fighting against insergency particularly in the Nirth East and North West. He maintained that the troops’ giant strides have led to the mass surrendering of terrorists and their family members in droves. Troops have also maintained this feat, through their operational engage

Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci ÆŠalibbai Su Maka ASUU Kotu

Kasancewar zaman tattauna tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da gwamnatin tarayya an tashi dutse a hannun riga, hakan ya fusata gwamnatin tarayyar Najeriya, in da aka jiyo Ministan Ilmin ƙasar, Malam Adamu Adamu na shawartar ɗaliban jami'ar da ke zaman jira a gida na su maka ƙungiyar a kotu. Ministan ya ce dukan alhakin ɓatawa ɗaliban lokaci ya rataye a wuyan malaman jami'a, kuma ya zama wajibi su biya ɗaliban diyya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta saka ƙafar wando guda da malaman ta hanyar ƙin biyansu albashin watannin da suka kwashe ba tare da aiki ba. Wasu daga cikin malaman jami'ar sun fara mayar da martani kan wannan matsaya ta gwamnatin tarayya. Dakta Mansur Isah Buhar, na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Na amice ɗari bisa ɗari cewa adalci ne kada a biya membobin ASUU albashinsu na tsawo wata shida da suka kwashe suna yajin aiki, saboda kuwa ai ba su yi aikin da ya dace a ce sun y

Hukumar Lura Da Kafafe Watsa Labarai Ta Najeriya Ta Ƙwace Lasisin Gidajen Rediyo Da Talabijin 52

Shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Illela ne ya sanar da hakan a yau jumu’a, in da ya bayyana cewa akwai É—imbin bashin da ya kai naira biliya 2 da rara da ake biyar gidajen talabijin na African Independent Television (AIT) da Silver Bird Television da aka fi sani da (STV) tare da Æ™arin wasu 52. Shugaban hukumar ya ce dokar Najeriya mai Lamba CAP N11, Sashe na 10, ta shekarar 2004 ta ba hukumar NBC wannan dama, kuma tun a watan Mayun bana ne suka wallafa sunayen kafafe watsa labaran da suka kasa sabunta lasisinsu tare da umurtar su da yin haka a cikin mako biyu rak, ko su fuskanci wannan mataki na karÉ“e mu su lasisi. Wannan matakin dai ana ganin shi ne irin sa na farko a tarihin Najeriya da ya shafi gidajen rediyo mallakar jahohi da masu zaman kansu. Kazalika, masana na fassara shi da wani salon gwamnatin tarayya na yaÆ™ar ‘yancin faÉ—ar albarkacin baki. Wasu daga gidajen rediyo da wannan dakatarwar ta shafa sun haÉ—a da Gidan Rediyon Rima na Sokoto da Rediyon Jahar K

Salman Rushdie Na Cikin Mawuyacin Hali

Tun  bayan da wani matashi a birnin New York na Amurka, mai suna Hadi Matar ya sokawa marubucin wuÆ™a ya ke kwance a wani asibiti a birnin. A jiya lahadi aka gurfanar da mista Mata a gaban wata kotu in da ya musanta laifukan yunÆ™urin kisan kai da ake zargin sa da yi. AlÆ™alin kotun Jason Schmidt ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shi ba tare da bayar da beli ba har zuwa lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotun. Wani makusancin Salman Rushdie mai suna Andrew Wylie, ya sanar da cewa  Mista Rushdie na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan da aka daÉ“a ma sa wuÆ™a a fuska da wuya da kuma cikinsa, abinda ya kai ga taÉ“a hantarsa. Kusan shekara 10 kenan Salman Rushdie na famar É“uya, tun daga lokacin da shugaban addinin Æ™asar Iran, Ayatullahi Ruhullah, ya bayar da umurnin a kashe shi tare da saka ladar dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sannan a shekarar 2012 gwamnatin ta Farisa ta Æ™ara wasu dala 500,000 bisa ga na farko. Fit

'Yan Jarida Na Shan ÆŠauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci É—aurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da Æ™asarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar Æ™asa, sakamakon É—aga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai É—auke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaÆ™i”. Gwamnatin Rasha ta daÉ—e tana É—aure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaÆ™in  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waÉ—anda aka samu da laifin watsa labarun Æ™arya  tsawon shekara goma a gidan jarum.

Cire Iyorchia Ayu Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Kasada Ce – Debo Ologunagba

A wani zaman sulhu da ake ci gaba da yi a Abuja, gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da tsohon mataimakain jam’iyar PDP na yankin kudu, Chif Olabode George, na cikin sahun gaba wajen ganin jam’iyar ta cire shugabanta na yanzu, Iyochia Ayu daga muÆ™aminsa muddin a na neman zaman sulhun ya kai ga haifar da É—a mai ido. A cewar su, hakan ne kawai zai iya samar da daidaito ga yankin kudancin Najeriya kasancewar ba adalci ne ba É—an takarar shugaban Æ™asa da shugaban jam’iya su fito a yanki guda ba. To, amma kuma wannan buÆ™ata ta gamu da cikas in da a yayin hirarsa da manema labarai a Abuja, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ba za ta saÉ“u ba, domin cire shi kasada ce, da za ta iya jefa PDP cikin sabon ruÉ—ani.  Ya Æ™ara da cewa, “ai a fili take Æ™arara, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar duk lokacin da aka cire shugaban jam’iyya a bisa kowane dalili ne kuwa, to mataimakinsa kan maye gurbinsa kuma ya zama sun fito daga shiya É—aya. Kazalika, kundin tsarin mulki

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. ÆŠaya daga waÉ—anda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI Sun Kai Samame Gidan Dold Trump

  Tsohon shugaban Æ™asar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa tawagar jami’an hukumar sun mamaye gidansa na alfarma da aka fi sani da suna Ma-a-Lago da ke a gaÉ“ar tekun jahar Fulorida. Rahotanni sun nunar da cewa samamen na da nasaba da wani bincike da ake kan gudanarwa da ke zargin Mista Trump da riÆ™e wasu muhimman takardun gwamanati tun bayan saukar sa daga mulki. Sai dai Mista Trump ya bayyana wannan mataki da kutsen da ya saÉ“awa doka, “Babu wani abu makamancin wannan da ya taÉ“a faruwa da Shugaban Amurka a tarihance”. Sashen adana bayanan gwamnatin Amurka ya sanar tun a farko cewa, Mista Trump bai miÆ™a wasu muhimman takardu ba da suka haÉ—a da wasiÆ™u da ya zama wajibi duk shugaban Æ™asa mai barin gado ya hannunta bayan barin sa mulki. Jami’an ofishin sun ce sun gano manyan akwatuna 15 a gidan waÉ—anda ke É—auke da muhimman takardun. Daga baya sashen adana bayanan ya shaidawa majalisar dokokin Amurka cewa kowace akwati da aka gano an yi mata alama

Gwamna Tambuwal Ya Umurci Malaman Jami'ar Sokoto Su Koma Aiki

Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya umurci Malaman Jami’ar  Jahar Sokoto da su koma bakin aiki ba da bata lokaci ba,bayan kwashe wata shida jami’ar na rufe  sakamakon yajin aikin Kungiyar Malamn Jami’a (ASUU). Wannan mataki na kama da bayar da umurnin nan take in da ya nuna matukar bacin ransa yadda malaman ke ci gaba da kauracewa wuraren aikinsu da zimmar bin umurnin kungiyar ta ASUU. Ya kuma nunar da cewa babu wani hakki da malaman jami’ar Jahar Sokoto ke bin gwamnatinsa kama daga albashi ya zuwa sauran bukatu da bai yi mu su ba. Ya bayyana cewa babu wata matsala a duniya da ta gagari tattaunawar da za ta kai ga cimma maslaha, kuma ya zama wajibi a fito da matakin da zai iya zama kandagarki ga duk wani abu da ke haifar da yajin aiki a Najeriya. “Bai kamata ku biyewa uwar kungiya ta ASUU ba, saboda matsalolinsu ba su shafe ku ba. Kuna cutar da dalibanku ne kawai, kuma wannan biyayyar da kuke  ci gaba da yi na da matukar muni da nakasu ga makomar ilmi; ina mai b

Kalubalen Tsaro Da Canza Shekar Kwamishinan Tsaron Jahar Sokoto

  A daidai lokacin da matsalar tsaro ke Æ™ ara ta’azzara a jahar Sokoto, kwamishinan tsaron jahar Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya bayar da sanarwar aje mu Æ™ aminsa tare da ficewa daga jam’iyyar jam’iyar PDP mai mulkin jahar. A cewar tsohon kwamishinan tsaron, “akwai gaggan matsaloli da suka taka rawa wajen ficewarsa daga jam’iyayar, da suka ha É— a da sakacin gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal na watsi da dukan   shawarwarin da ake ba shi da suka shafi tsaro; kazalika da rashin sauraren Æ™ orafe- Æ™ orafen dangane da ci gaban jahar a fannoni da dama”. A ranar alhamis da ta gabata dai wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a garin Chakai da ke Ƙ aramar Hukumar Mulki ta Tambuwal, wadda ita ce mahaifar gwamnan jahar, in da suka sace mutum goma sha bakwai ciki har da mata da Æ™ ananan yara, tare da neman diyyar naira miliyan takwas da dubu É— ari biyar. Kazalika, sun fitar da sanarwar shirin hallaka mutanen daga gobe talata, muddin ‘yan uwan wadanda ake garkuwa da sun ba su aika mu su ku

INEC Ta Yi Watsi Da Lawan Ta Tabbatar Da Machina

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta Najeriya (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa a jiya alhamis 23 ga watan Yuni, 2022 da ke tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar dattijai na kasa mai wakiltar kananan hukumomin Machina da Gashuwa da Nguru da Jakusko da Yusufari da Bade da kuma Karasuwa jahar Yobe, in da kuma ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ta san da wani zaben fidda gwani da aka gudanar ba koma bayan wanda ya wakana a ranar 28 ga watam Mayu. A cewar INEC babu wani dan takara da ta sani face Bashir Sheriff Machina. Tun da farko dai Sanata Ahmad Lawan ne ke wakiltar wadannan kananan hukumomin, wanda hukumar ta bayyana da cewa ya nemi mukamin shugaban kasa a maimakon matsayin da ya ke akai yanzu haka na dan majalisar dattijai. An dai jiyo shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, a wata hira da sashen Hausa na BBC na bayyana cewa ba su san da wani ba sai sanata Ahmed Lawan, abinda ya jawo cece-ku-ce.

An Kama Wasu Daliget Da Kuri'un Bogi

Har yanzu ana ci gaba da jefa kuri'a kuma kimanin jaha 14 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaben fidda gwani na APC da ke gudana a Dandalin Eagles da ke Abuja. Wadannan jahohin su ne Abia da Kano da Katsina da Adamawa da Delta da Cross River da Osun da Ogun da Borno da Neja da Binuwai da sauran su. Zuwa tsakar daren jiya an dan samu tsaiko na awa guda kasancewar an samu wasu daliget da kuri'un bogi, wanda aka dakatar da zaben kafin daga baya a ka ci gaba.

Yahaya Bello Ya Caccaki Buhari

Da ya ke jawabi a lokacin da ake gudanar da shirin zaben fitar da gwani, gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya nemi a zabe shi domin ya magance matsalar tsaro da karancin ilmi da ake fama da su yanzu haka a Najeriya. Ya ce, "akwai takaici ace wai yanzu malaman jami'a suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune a gida kuma an kasa magance wannan matsala mai saukin magancewa". Yahaya Bello wanda ya ce ba zai jaye ma kowa a neman tikitin shugaban kasa, ya kara da cewa shi matashi ne kuma matasa ya kamata a ba dama su mulki kasar nan ba tsofaffi da suka gaji ba. Ya yabawa shugaba Buhari akan saka hannu a kan dokar ba matasa damar tsayawa takara, in da ya ce abu ne mai kyau. Ya yi kira ga mata da sauran 'yan Najeriya da ya ce ana zalunta da su zabe shi. Dan takarar ya ce "yanzu haka babu tsaro ko kadan kuma an kyale, ana kashe mutane ana kona mu su dukiya kuma ana kallo an zura ido".

'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Fara Janye Ma Bola Tinubu

Kawo yanzu dai akwai masu neman mukamin shugaban kasa da suka fito kafin fara jefa kuri'a suka bayyana cewa sun janye takararsu kuma sun marawa tsohon gwamnan jahar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Daga cikin su akwai gwamnan jahar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar da Fayemi Kayode da Ajayi Boroffice da tsohon kakakin majilasar wakilai Dimeji Bokole da kuma Gidein Akpabio. Amma Pasto Tunde Bakari ya bayyana cewa shi kam ba zai jaye ma kowa da ga cikin 'yan takara ba, kasancewar "ba su da kyakkyawar manufar gina kasa face rusa ta", in ji shi. Akwai 'yan takara da dama da ya zu haka su ke jiran a fara kada kuri'a da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Ahmed Yariman Bakura da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rotimi Amechi da sauran su. Zamu kawo mu ku karin labari nan gaba.

"Ba Ni Goyon Bayan Kowane Dan Takara" - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bauyana cewa bai zabo kowane dan takara ba, akan haka a bar daliget su zabi wanda 'yan jam'iyya ke so. Bayan ganawa da shugaban kasan jim kadan bayan da shugaban jam'iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudo, sun ce sun tabbatar ma shugaba Buhari cewa har yanzu suna kan bakansu na mika mulki ga kudu. Wannan dai ya nuna daga gobe takara jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Gwamnonin APC Da Sauran Masu Takara Ba Su Amince Da Zabin Ahmad Lawan Ba

Gwamnonin jam'iyar APC da masu takarar neman mukamin shugaban kasa sun ja daga akan wannan mataki na tsayar da Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sun nemi dole mulki ya koma kudu kuma a gudanar da zaben fidda gwani. Labarin da ke shigowa yanzu haka ya nunar da cewa za a fafata a zaben fidda gwani tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi da David Umahi da sauran su a Dandalin Eagles da ke Abuja a gobe talata. Za ku ji sauran bayani daga baya.

Stepping Down Not The Right Option - Osinbajo

Vice president Yemi Osinbajo has denied reports that he intends to step down for a certain presidential aspirant ahead of the presidential primary of the All Progressives Congress (APC). The denial is contained in a statement by the chairman of Osinbajo’s campaign council, Richard Akinnola on Sunday. According to the statement, the people behind the speculation are “afraid of the huge political support base of the Vice President, Prof. Yemi Osinbajo,” adding that the VP is ready for the presidential primary scheduled to hold between June 6 and 8. The campaign council “welcomes our distinguished delegates from across the country to Abuja for our presidential primaries. “As you settle down in Abuja, we implore you to kindly disregard various fake news making the rounds that Prof. Yemi Osinbajo has stepped down. “Osinbajo would be hoping to clinch the ticket of the ruling party with much desire to take over from his principal, President Muhammadu Buhari at the end of his tenur

Gwamnatin Buhari Ta Ce Za Ta Samar Da Hanyar Saukar Da Farashin Abinci

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fara lalubo zaren kawo karshen matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Ministar ta ce za a fito da wata hanyar yin taron kasa da masu ruwa da tsaki domin samar da matakin da za a dogara gare shi wajen rage ma 'yan kasa radadi cikin gaggawa. Idan ana iya tunawa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kulle kan iyakokin kasar da zimmar bunkasa noma abinda ya haifar da tsananin tsadar abinci.

PDP Na Son Sake Zaben Fidda Gwani A Jahar Bauchi

Rahotanin da ke shigowa yanzu haka na cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar PDP a jahar Bauchi in da jam’iyar ke shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jahar. Wannan ya biyo bayan matakin da  Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya dauka ne, da ya kekasa kasa ya ce ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba. Jaridar Daily Trust da DW Hausa duka sun ruwaito wannan labari.

Abubakar Gada Da Salame Sun Janye Daga Zaben Fidda Gwanin APC A Sokoto

Sanata Abubakar Gada da Abdullahi Balarabe Salame sun fitar da sanarwar janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamna a jahar Sokoto bayan wata takaddama da ta biyo baya. Takardar da suka fitar ta bayyana cewa tun farko sun nemi a yi zaben ta hanyar 'yar tinke, amma kuma wani bangare na jam'iyyar ya yi watsi da wannan. Sun ce ganin ba za a yi mu su adalci ba ya sa ba za su shiga zaben ba, kuma suna kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta duba yuwar bin bukatar da suka nema tun da farko. A cewar takardar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa duk zaben da aka yi ba tare da amfani da masu zaben 'yan takara da aka fi sani da delegate, ko kuma ta hanyar sulhuntawa ba to haramtacce ne. Kan haka suke neman uwar jam'iyyar da ta san dacewa ba a yi zabe a jahar Sokoto ba, kuma wannan zai iya jawo jam'iyyar APC ta rasa dan takara, in ji su.

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura

Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a. Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari. Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023. Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai d

Gwamnatin Jahar Sokoto Ta Sanya Dokar Hana Yawo Tsawon Sa'a 24

Gwamnatin jahar Sokoto ta bayar da sanarwar saka dokar hana yawo a birnin Sokoto da wasu sassan jahar na tsawon sa'a 24. Ofishin mai ba gwamna shawara akan lamurran watsa labarai ne ya fitar da wannan sanarwa ranar asabar 14/05/2022. A cewar sanarwar, an dauki matakin ne don samar da zaman lafiya a jahar. Wannan nan dai na zuwa ne lokacin wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin na Sokoto, wanda ke da nasaba da kamen da 'yan sanda suka yi na mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Debirah Samuel Yakubu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari kwana biyu da suka gabata. In da da farko zanga-zangar da aka soma ta lumana ta rikide zuwa kone-kone. In da masu zanga-zangar suka cika harabar Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III.

An Kashe Wata Daliba Da Aka Zarga Da Batanci Ga Manzon Allah A Jahar Sokoto

Wata dalibar Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, mai suna Debora Samuel, ta gamu da ajalinta lokacin da wasu matasa da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka kashe ta hanyar kona ta, bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi mai tsira da amincin Allah. Lamarin ya kazance ne bayan da wasu daga daliban kwalejin suka yi zargin cewa ta dade ta na wannan batancin abinda ya kai ga barkewar rikicin da ya kai ga salwantar ranta. Tuni dai mahukuntan jahar Sokoto suka bayar da sanarwar rufe kwalejin har a kammala bincike. Babban sakatare a ma'aikatar ilmi mai zurfi ta jahar Sokoto Alhaji Almustapha Usman Ali, ya shaidawa manema labarai cewa, an bayar da umurnin rufe kwalejin kazalika za su sanar da jama'a mataki na gaba idan har an kammala bincike. An dai girke jami'an tsaro a harabar makarantar domin dakile rikicin da ka iya tasowa. Tuni dai da hotunan bidiyo da Tantabara ba ta kai ga tantantace sahihancinsu ba, suka karade shafukan sada zumunta, wadanda k

Daliban Jahar Sokoto Ba Zasu Rubuta Jarabawar WAEC Ba

Hukumar Shirya Jarabawar Sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta bayyana cewa jahohin Sokoto da Zamfara ba su aike mata da sunayen dalibansu da za su rubuta jarabbawar kammala babbar sakandire ba, wadda za a soma tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga watan Yunin gobe, kamar yadda sakataren hukumar shirya jarabawar Mista Patrick Aregan ya fitar da sanarwa. Sai dai a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ilmi na jahar Sokoto Bello Abubakar Guiwa, ya ce matsalar ba daga gare su ba ne.  Kwamishinan ya ce hukumar ta WAEC ta fito ne da wani tsari na sun amsar kudi ba gaira ba dalili gare su wanda ya sa suka yi watsi da ita. Ya kara da cewa suna da dalibai kusan 30,000 da zasu rubuta jarabawa a wannan shekara, to amma sai hukumar hana su lambobin jarabawar da ake rabawa dalibai ta kuma ce duk wani kuskure daya da aka samu akan kowane dalibi, wajibi ne sai an biya naira 5000, wanda kuma miliyoyin kudade ne, kazalika sai gwamnatin jahar Sokoto ta biya kashi 40 cikin dari kafin som

ASUU Ta Tsunduma Sabon Yajin Aikin Watanni Uku

Kungiyar Malaman Jami'a ASUU ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau litinini 09/05/2022 da ta bayyana sake tsunduma wani sabon yajin aikin makonni 12. ASUU ta bayyana rashin gamsuwa da yadda bangaren gwamnatin tarayya ya dauki lamarin ba tare da muhimmanci ba. Sanarwar ta ASUU ta kuma nunar da yadda gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure yarjejeniyar da suka yi a 2020, tare da cewa babu wata alamar gwamnati da gaske ta ke. Kungiyar Malaman Jami'ar dai ta kwashe wata hudu tana yajin aiki kafin sake saka wani sabon wa'adi a yau na tsawon makonni 12 abinda masana harkar ilmi ke cewa ya gurgunta sha'anin ilmi a Najeriya.

Zan Yi Amfani Da Kundin Tsarin Mulki Ba Alkur'ani Ba - Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jahar Zamfara sanata Sani Yariman Bakura ya ayyana manufarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC. A wata hira da BBC Hausa Yariman Bakura ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsaloli uku da zai mayarwa hankali idan aka zabe shi, da suka hada da tsaro da jahilci da talauci. Da aka tambai shi ko bai ganin wadanda ba musulmi ba na iya dari dari a zabensa. Sai ya ce a yanzu kam sabanin wancan lokaci da aka sani da kundin tsarin mulki zai yi amfani wajen rantsuwar kare Najeriya. Ya kuma kara da cewa a lokacin kaddamar da manufar tsayawarsa takara akwai limaman kiristoci daga Zamfara da wasu wurare a Najeriya da suka halarta, wanda alama ce da ke nuna zai yi ma kowa adalci a cewar sa. Sanata Sani Yariman Bakura dai shi ne gwamna na farko da ya assasa shari'ar Musulunci a jahar Zamfara a shekarar 2000. Wanda daga baya aka samu jahohin Sokoto da Kano suka bi sahu.  Abinda ya jawo karo na farko a tarihi gwamnatin jahar Zamfara ta

Rasha Na Shirin Kai Ma Amurka Da Kawayenta Hari

Reuters Rasha ta gargadi kasashen yammacin duniya da cewa za a dauki tsauraran matakin soji kan duk wani hari da za a kai a yankin na Rasha, tana mai zargin Amurka da manyan kawayenta da zagon kasa ga tsaron kasashen Turai ta hanyar tunzura Ukraine a fili ta kai wa Rasha hari. Yunkurin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya raba wasu miliyoyi da matsugunansu, ya kuma haifar da fargabar kazamin fada mafi muni tsakanin Rasha da Amurka, tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuba a shekara 1962. Watanni biyu tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, a cikin 'yan kwanakin nan Rasha ta ba da rahoton wani jerin hare-haren da sojojin Ukraine suka kai a yankunan Rasha da ke makwabtaka da Ukraine, kuma ta yi gargadin cewa irin wadannan hare-haren na da hadari sosai. Ukraine ba ta dauki alhakin kai tsaye ba, amma ta ce abubuwan da suka faru na mayar da martani ne, yayin da Rasha ta yi kakkausar suka ga kalaman da kungiya

Ba Mu Yarda Da Sulhu Ba - Tambuwal

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi watsi da sakamakon taron da aka yi na amincewa da mutum daya da zai tsaya takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a 2023. Gwamna Tambuwal ya yi watsi da hakan ne ta hannun daya daga cikin kungiyoyin yakin neman zabensa, Tambuwal Campaign Organisation (TCO). A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Daraktanta, Nicholas Msheliza a ranar Juma’a ta ce “Ofishin Kamfen din Tambuwal (TCO) ya ja kunnen wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar da za zabi daya a matsayin maslaha daga cikin mu hudu, kuma wannan karya ce tsagwaronta sannan ba daidai ba ne “Gaskiyar lamarin ita ce kungiyar ta hadu a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, inda suka yi taron bita;  kuma, gaba É—aya sun yarda cewa tsarin yarjejeniya ba ya a

NDE Disbursed 20,000 Naira as Loan to 228 Small Scale Business Owners in Sokoto

The National Directorate of Employment (NDE) has disbursed simple rate loan of =N=20,000 to 228 small business owners in Sokoto State.   Speaking on the occasion, held Thursday, at Shamsuddeen Plaza Sokoto, the State Coordinator, Mrs Eunice J. Danmallam said the NDE was established in 1987, and since then it has continued its creative work especially for young graduates and always keeps providing training and support to small business owners.  She added that under the current Director General of the NDE, Malam Abubakar Nuhu Fikpo, a number of measures have been put in place to help youths and small scale business owners by lending them low interest loans to repay within three months.   However, Danmallan said the agency has selected about 8026 Nigerians to benefit from the Programme, of which 228 are from Sokoto State.  The Sokoto State Coordinator urged the beneficiaries of the scheme to use the loans wisely, and then demanded that they repay after three months

Abdul'aziz Yari Zai Koma PDP

A yanzu daga kowane lokaci wata majiya mai tushe ta sanar da cewa jagoran jam'iyyar APC a jahar Zamfara, kuma tsohon gwamnan jahar, Abdul'aziz Yari zai bar jam'iyyar APC zuwa PDP. Tantabara News za ta kawo cikakken. Labarin nan gaba. KUNA IYA KARANTA:  http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/sabon-rikici-bangaren-abdulaziz-yari-ya.html

Shugaban Gwamnatin Jamus Frank-Walter Steinmeier Na Shan Suka

Jami'an Ukraine da na Poland sun soki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da cewa yana dasawa da  Rasha. Jakadan Ukraine a birnin Berlin ya kaurace wa wani bikin zaman lafiya da mawakan Rasha da Steinmeier ya shirya. Gidan rediyon DW ya ruwaito cewa, Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk da mataimakin firaministan Poland Jaroslaw Kaczynski  sun caccaki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier sakamakon alakar da aka lura yana da ita da kasar Rasha. Melnyk ya gaya wa jaridar Tagesspiegel cewa, "Steinmeier na da abin da ya ke boyewa dangane da wannan alaka tasa da Rasha". Ya kara da cewa, "mutanen da ke da alaka da Steinmeier kamar Jens Plötner, mai ba wa Wazirin Jamus, Olaf Scholz shawara kan manufofin kasashen waje, da Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus Andreas Michaelis hadi da karin wasu, na daga cikin wadanda ake zargin cewa ba za su rasa hannu ga wannan kusanci ba". Kaczynski ya kuma bayyana cewa manufofin ketare na Jamus na da tasg