Gwamnatin jahar Sokoto ta bayar da sanarwar saka dokar hana yawo a birnin Sokoto da wasu sassan jahar na tsawon sa'a 24.
Ofishin mai ba gwamna shawara akan lamurran watsa labarai ne ya fitar da wannan sanarwa ranar asabar 14/05/2022. A cewar sanarwar, an dauki matakin ne don samar da zaman lafiya a jahar.
Wannan nan dai na zuwa ne lokacin wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin na Sokoto, wanda ke da nasaba da kamen da 'yan sanda suka yi na mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Debirah Samuel Yakubu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari kwana biyu da suka gabata.
In da da farko zanga-zangar da aka soma ta lumana ta rikide zuwa kone-kone. In da masu zanga-zangar suka cika harabar Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Comments