Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF. Lula ya yi waÉannan kalamai a wata ziyarar aiki da ya kai Chana, jiya Alhamis a birnin Shanghai a wani bikin kaddamar da takwaransa, Dilma Rousseff a matsayin sabuwar shugabar bankin raya kasashen BRICS, da gamayyar kasashenn Brazil da Rasha da Indiya da Chana da kuma Afirka ta Kudu suka samar. "Me ya sa kowace Ęasa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuÉin duniya?" Ya Ęara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuÉin da zai gudanar da hulÉar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran Ęasashen duniya? Ya ce yana mamakin yadda Ęasashe cike da rauni su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuÉaÉensu. A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya ...