Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2021

Kasar Isra'ila Na Kaiwa 'Yan Jarida Hari

 GAZA: Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya lalata wani dogon gini a birnin Gaza wanda ke dauke da ofisoshin kamfanin dillacin labarai na Associated Press da sauran kafafen yada labarai a yau Asabar, wannan farmakin sojin ya zo ne kwatsam ba tare da yin gargadi ga mazauna ginin ba, matakin da sojoji suka dauka na yin shiru a yayin fafatawarsu da kungiyar Hamas. Harin ta sama ya zo ne kasa da sa'a guda bayan da sojojin suka umarci mutane su fice daga ginin, wanda kuma ya hada da Al-Jazeera, da sauran ofisoshi da gidajen jama'a. Karfin harin ya ruguje daukacin ginin mai hawa 12, qanda ya haddasa turnukewar Æ™ura.  Babu wani bayani akan dalilin da ya sa aka kai harin.   Wannan sabon farmakin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani harin sama da Isra’ila ta kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke da yawan jama’a a garin na Gaza da ya kashe Falasdinawa akalla 10 'yan asalin dangi daya, wadanda galibinsu kananan yara ne, a wani hari mafi muni da aka kai a rikicin da ke

Israel Targets Journalists

GAZA: An Israeli airstrike destroyed a high-rise building in Gaza City that housed offices of The Associated Press and other media outlets on Saturday, the latest step by the military to silence reporting from the territory amid its battle with the militant group Hamas. The strike came nearly an hour after the military ordered people to evacuate the building, which also housed Al-Jazeera, other offices and residential apartments. The strike brought the entire 12-story building down, collapsing with a gigantic cloud of dust. There was no immediate explanation for why it was attacked. The strike came hours after another Israeli air raid on a densely populated refugee camp in Gaza City killed at least 10 Palestinians from an extended family, mostly children, in the deadliest single strike of the current conflict. Both sides pressed for an advantage as cease-fire efforts gathered strength. The latest outburst of violence began in Jerusalem and has spread across the region, with

Wata Mota Cike Da Harsasan Bindiga Ta Fada Rami A Garin Awka Na Jahar Imo

Hankalin jama'a yayi matukar tashi a jiya Lahadi biyo bayan gano wata babbar mota cike da harsasai masu rai a birnin Anacha na jahar Imo da ke kudu maso gabashin tarayyar Najeriya. Rahotannin da suka shigo muna na cewa jami'an tsaron cikin hanzari sun afkawa garin na kasuwanci domin daukar matakin gaggawa kan lamarin.  Babbar motar wadda ke dauke da kwaliyoyin harsasai masu rai ta fada cikin wani rami da ke kan titi, inda dukan harsasan suka zube. Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce: “Motar ta fadi, kuma duk titin na cike da harsasai.  Wasu yaran ma sun debi wasu da hannayensu suka gudu, kafin jami’an tsaro su iso wurin. ”  Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa direban babbar motar da mai yi masa hidima sun yi watsi da motar bayan hatsarin ya faru, inda suka yi batan dabo zuwa inda ba a sani ba. Amma wata majiyar ta ce ‘yan sanda sun cafke direban. “Lamarin ya jawo jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin hanyar Awka da da safiyar yau. 'Yan sanda sun