Skip to main content

Wata Mota Cike Da Harsasan Bindiga Ta Fada Rami A Garin Awka Na Jahar Imo

Hankalin jama'a yayi matukar tashi a jiya Lahadi biyo bayan gano wata babbar mota cike da harsasai masu rai a birnin Anacha na jahar Imo da ke kudu maso gabashin tarayyar Najeriya.

Rahotannin da suka shigo muna na cewa jami'an tsaron cikin hanzari sun afkawa garin na kasuwanci domin daukar matakin gaggawa kan lamarin.
 Babbar motar wadda ke dauke da kwaliyoyin harsasai masu rai ta fada cikin wani rami da ke kan titi, inda dukan harsasan suka zube.

Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce: “Motar ta fadi, kuma duk titin na cike da harsasai.  Wasu yaran ma sun debi wasu da hannayensu suka gudu, kafin jami’an tsaro su iso wurin. ”

 Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa direban babbar motar da mai yi masa hidima sun yi watsi da motar bayan hatsarin ya faru, inda suka yi batan dabo zuwa inda ba a sani ba.
Amma wata majiyar ta ce ‘yan sanda sun cafke direban.

“Lamarin ya jawo jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin hanyar Awka da da safiyar yau. 'Yan sanda sun fara isa yankin kafin sojoji su zo. 
Daga baya suka kawo tifa, kuma suka yi amfani da motar daga kaya don dibar harsasan.

 “Tifar dai ta yi tafiya sau uku don daukar duka harsasai zuwa inda ba a sani ba kafin daga bisani a fitar da motar daga cikin ramin,” in ji majiyar.

 Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, lokacin da aka tuntube shi, ya musanta labarin faruwar lamarin, yana mai cewa zai gano.
PPRO bai amsa ba kamar yadda yayi alkawari kawo lokacin hada wannan rahoton.

Comments