Skip to main content

Posts

Showing posts from March 24, 2022

Kotu Ta Tabbatar Da Isah Sadik Achida Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jahar Sokoto

Babbar kotun daukaka kara ta kasa mai mazauninta a Abuja ta tabbatar da Alhaji Isah Sadik Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jahar Sokoto. An dai shafe wata daya ana jayayya a kotu tsakanin Alhaji Isah Sadik Achida da bangaren Mainasara Abubakar da ke tare da Alhaji Abdullahi Salame sai kuma bangaren shugaban majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida. Idan ana iya tunawa dai babban mai saka kara na kasa kuma ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami SAN, ya taba wani ikirari na cewa kotu za ta tabbatar da shugabancin ga Mainasara Abubakar da ke bangaren Hon. Abdullahi Salame, wanda wannan hukuncin ya zama tamkar watsa kasa a fuskar ministan shari'ar da ya yi riga malam masallaci gabanin hukuncin kotu.

Sabuwar Dambarwar Shugabancin APC

Kwana biyu kafin ta gudanar da babban zabenta na kasa, jam'iyyar APC ta sake tsunduma wata sabuwar turka-turka game da makomar wanda za a zaba matsayin sabon shugabanta. A wata hira da BBC Hausa, gwamnan jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudo, wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin APC na kasa ya ce yanzu haka sun kasa cimma matsaya akan wanda zai zama shugaban jam'iyyar a ranar asabar mai zuwa. Bagudo ya kara da cewa sun gana da shugaba Muhammadu Buhari akan samar da matsaya, amma kuma sun lura cewa da wuya idan ba zabe za a gudanar ba a maimakon samar da maslaha. Da aka tambai shi ba ya ganin samar da maslaha tamkar an tilastawa wani ne bin abinda ba ya so, shugabana kungiyar gwamnonin ya ce zai yuwu a sulhunta amma idan hakan ta gagara za a bi hanyar da za ta kawo mafita. Sai dai bai yi cikakken bayani akan wace hanya ce da za a bi idan har an kasa yin sulhu tsakanin 'yan takara. Ga alama wannan na nuna irin yadda jam'iyyar za ta fuskanci kalubale gabanin ko ba