Skip to main content

Posts

Showing posts from February 6, 2021

An Ruguza Makarantar Malam Abduljabbar Kano

Dazu dazun nan gwamnatin jahar Kanon ta tura jami'an ma'aikatar lura da tsarin filaye in da ta ruguza makarantar Malam Abduljabbar. Gwamnatin dai ta taba bayyana cewa filin da ya ke amfani da shi haramtacce ne, in da ta kai ga kwace shi tare da bada umurnin gudanar da wasu muhimman ayukka a wurin. Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin jahar Kano da Abduljabbar in da a ranar laraba sakataren watsa labaran gwamnatin jahar, Muhammad Garba ya bayar da sanarwar rufe masallacin Malam Abduljabbar tare da hana masa gudanar da wa'azi baki daya. In da ta ce hakan na da alaka da irin yadda ya ke tunzura jama'a a kalaman da ya ke amfani da su a lokacin da ya ke da'awa.

TAURARUWA MAI WUTSIYA... GANDUJE KO ABDULJABBARI?

RA'AYI: Dambarwar da ta dabaibaye batun nan na dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara a jahar Kano na ta jan hankalin al'umma a kwanan nan. Lamarin ya ja ra'ayin masana da masu sharhi na ta tofa albarkacin bakinsu kan batun. Wannan ya sa jaridar Tantabara News ta yi tsokaci akan yadda masana da tarihi ya hango makomar irin wadannan mutane. A ranar larabar makon jiya ne gwamnatin jahar Kano ta dauki matakin rufe masallacin da malamin ke da'awa da aka fi sani da suna As-habul Kahf da ke takiyar birnin Kano. Haka ma gwamnatin ta hana ma sa yin da'awar tare da yi ma sa wani abu mai kama da daurin talala; da ta bayyana da cewa kandagarki ne ga irin matakan da aka lura ya na dauka na hargitsa jama'a tare da boyayyar manufa mai jirwaye kama da wanka.   Wanene Abduljabbar Nasir Kabara?  Abduljabbari dai matashin malami ne mai dimbin magoya baya, mai son daukaka da suna a kafofin sada zumunta na zamani da kafar sadarwa ta YouTube mai kare mashabar Shi'a aka...