Skip to main content

An Ruguza Makarantar Malam Abduljabbar Kano

Dazu dazun nan gwamnatin jahar Kanon ta tura jami'an ma'aikatar lura da tsarin filaye in da ta ruguza makarantar Malam Abduljabbar. Gwamnatin dai ta taba bayyana cewa filin da ya ke amfani da shi haramtacce ne, in da ta kai ga kwace shi tare da bada umurnin gudanar da wasu muhimman ayukka a wurin.
Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin jahar Kano da Abduljabbar in da a ranar laraba sakataren watsa labaran gwamnatin jahar, Muhammad Garba ya bayar da sanarwar rufe masallacin Malam Abduljabbar tare da hana masa gudanar da wa'azi baki daya. In da ta ce hakan na da alaka da irin yadda ya ke tunzura jama'a a kalaman da ya ke amfani da su a lokacin da ya ke da'awa.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.