Skip to main content

Posts

Showing posts from February 19, 2021

Shak Ahmad Gumi Ya Fara Tattaunawa Da wadanda Suka Sace Yaran Makarantar Kagara

Malamin ya sanar da cewa maharan da suka sace daliban wata Makaranta da ke Kagaran jahar Naija, sun kira shi domin ya nemo gwamnati a tattauna yadda za a saki yaran. Shak Ahamd Gumi ya ce, shi kan sa bai san in da maharan ke fakewa ba, amma dai ya samu tattaunawa ta waya da shugaban 'yan fashin da suka addabi yankunan arewacin Najeriya, mai suna Dogo Gide, in da ya sanar da malamin alkawarin da suka dauka na tattaunawa da gwamnati. To amma kuma har yanzu bangaren gwanatin tarayya da ma jahohi ba su ce uffan ba kan wannan batu. Duk dai kokarin da jami'an tsaro na gano in da wadannan mahara ke fakewa a dazuka ya ci tura, amma a galibin lokuta Shak Ahmad Gumi ya sha kutsa kai a dazuka da zimmar ilmantar da su da kuma nan shiga tsakani don neman sulhu.  Sai dai a duk wannan kokari da Ahmad Gumi ya nuna yana yi hare-haren 'yan bindiga sai karuwa suke, inda wannan kwashe dalibai a makarantun kwana shi ne na hudu baya ga makarantar Kankarar jahar Katsina kimanin watann