Samudawa su ne mutanen Annabi Saleh (AS) waÉanda ke da girman jiki da tsawo tamkar bishiyar dabino. WaÉannan wasu daga gidajen Samudawa ne da suka rage a halin yanzu. Ana kiran wajen da suna (Madaāin Salih) ko Al-Hijr da Larabci, (Ł±ŁŁŲŁŲ¬ŁŲ±āā). Yankin na nan a Al-āUla cikin lardin Madina a Hejaz, ta Ęasar Saudiyya. A shekarar 2008, Hukumar Kula Da Adana Kayan Tarihi Ta Majalisar Ęinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana Madaāin Salih a matsayin wani wajen da take girmamawa, wurin tarihi na Hegra na nan nisan kilomita 20 arewa da garin Al-āUla, tafiyar mil 250 arewa maso yammacin birnin Madina. Samudawa sun wanzu shekaru Éari bakwai da goma sha biyar kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Mutane daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci wurin, domin ganin ikon Allah.