Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ziyarci yankunan Ukraine da aka mamaye a karo na biyu tun bayan ƙaddamar da wani gagarumin farmaki, kamar yadda fada Kremlin ta sanar a yau Talata.
Putin ya ziyarci hedkwatar soji a yankin Kherson na kudancin ƙasar Ukraine da kuma hedkwatar tsaron Rasha da ke yankin Luhansk.
Tafiyar ta zo ne a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare a gabashin Ukraine.
Jaridar ƙasar Rasha taThe Moscow Times https://www.themoscowtimes.com/2023/04/18/putin-visits-occupied-ukraine-territories-a80862 ta bayyana cewa Fadar Kremlin ba ta bayyana takamaiman lokacin da tafiyar ta gudana ba kuma hotunan ziyarar biyu sun nuna Putin sanye da tufafi daban-daban.
Comments