Rikicin jamāiyar PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya na cikin kwale-kwale tun bayan da aka zabi gwamnan jahar Oyo Seyi Makinde jamāiyar PDP ke ganin ya na uwa da makarbiya a dukan lamurran da suka shafi jamāiyar, abinda suka ce na neman mayar da hannun agogo baya; kuma lamarin da wasu shuwagabannin jamāiyyar ke ganin shisshigi ne da kuma tare hanyar wasu. A baya bayan nan gwamna Makinde ya dinga kai kawo a rikicin jamāiyar a jahar Ikiti da ya ce neman sulhu ne da shiga tsakani, amma hakan ya kai ga musayar yawu tsakaninsa da gwamnan jahar Peter Fayose na lokacin, wanda ke yiwa gwamnan jahar Oyon kallon mai goyon bayan Sanata Abiodun Olujinmi da ya tsaya takara tare da shi. A halin yanzu an ji gwamnan na jahar Oyo na kurari da nuna goyon baya akan shari'ar da ake yi wa Fayose, in da Makinde ke ganin ya dace Hukumar Yaki da Zarmiyar Dukiyar Alāumma ta EFCC ta ci gaba tuhumar tsohon gwamnan jahar Ikitin. Rahotanni sun ce an jiyo shi ya na cewa...