Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2021

An Gano Wani Rini Na Zamanin Annabi Dawuda

Wata jaridar kasar Isra'ila mai suna Hamodia ta wallafa labarin mai ban mamaki da ya ja hankalin duniya a makon nan. Masu hakar kayan tarihi da hadin guiwa da Jami'ar Barllan da kuma Jami'ar birnin Tel-Aviv ne suka samu nasarar gano wannan rinin mai lainin shudi, da shuni hade da saheti da aka ce ya kai shekaru dubu daya kafin bayyanar annabi Isa (a.s.) da kuma mazauna wani kwari da ake kira Slaves Hill da ke lardin Timna ke rinawa a lokacin. Wani masani na Jami'ar Barllan Dakta Naama Sukenik da Dakta Erez Ben-Yosef, sun bayyana cewa rinin, mai matukar darajar gaske an samar da kayan hadinsa ne daga kwanson dodon kodi. Kuma an wallafa bayanin a mujallar PLOS ONE .

'Yan Bindiga Sun Sako Hakimin Radda Alhaji kabir Umar

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka, na cewa maharan da suka sace hakimin Radda, Alhaji Kabir Umar sun sako shi. Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da sakin nasa, sai dai ba ta yi cikakken bayanin yarjejeniyar da aka cimma kafin sakin sa ba. A ranar 22 ga wannan watan na Janairun makon jiya dai ne maharan suka sace ce shi daga Katsina zuwa dajin Zamfara. 'Yan bindigar sun sako shi a daren jiya bayan kwana hudu da sace shi. Rahotanni sun ce jami'an gwamnatun jahar Katsina da hadin guiwa da jami'an tsaro sun samu tattaunawa da maharan, abinda ya kai ga sakinsa, sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin na sa ba.

Sabuwar Kwayar Korona Ta Bulla A Najeriya

A halin yanzu da duniya ke tsakiyar fargaba da rashin sanin makoma, Hukumar Yaki Da Cuta Mai Yaduwa ta NCDC da ke Najeriya, ta fitar da sanarwar barkewar sabon nau'in cutar annobar korona da aka lakabawa suna B.1.1.7. Wannan sabuwar kwayar cutar dai ta fi ta farko saurin yaduwa da matukar hadari wajen kashe mutane, da aka tabbatar da ta kan yadu da kashi 70 cikin dari fiye da na farkon. A watan Disamban 2020 aka samu rahoton bullar sabuwar koronar a kasar Burtaniya da Afirka ta Kudu. Shugaban hukumar NCDC ta kasa Chikwe Ihekweazu ya sanar da hakan a jiya. Ya bayyana cewa hukumar za ta kara azama don yin kandagarkin bazuwar sabon nau'in korona na B.1.1.7 tsakanin jama'a. Wani kwararren likitan Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai suna Patrick Vallance, ya bayyana cewa, "daga marasa lafiya 'yan tsakanin shekaru 60 zuwa sama da suka harbu da tsohuwar kwayar cutar a kasar, 10 kan rasa rayukansu a cikin mutum 1000 kowace rana, amma a wannan karon, da wan

An Rantsar Da Shugaba Joe Biden

An rantsar da shugaban Amurka na 46 Joe R. Biden tare da mataimakiyarsa Kamala Harris. Shugaba Biden ya nemi goyon bayan Amurkawa wajen samar da hadin kan kasa. "Ina neman hadin kan ku wajen ci gaba da ginin dimukuradiyarmu mai shekaru fiye da dari biyu ta ci gaba", in ji Biden. Ya kara da cewa, "Fatan da na sa gaba idan na shiga ofis, shine tabbatar da Amurka ta dore a yadda a ka santa, da inganta huldar dangantaka tsakanimu da waje, yaki da korona hadi da tabbatar da Amurka ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa". Shahararriyar mawakiyar nan, Lady Gaga ce ta rera taken kasar, haka ma mawakiya Jennifer Lopez ta nishandantar da mahalarta bukin. An dai gudanar da bukin cikin tsauraran matakan tsaro. Tun da safiyar yau tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bar fadar White House cikin wani jirgi mai saukar ungulu in da ya nufi jahar Florida. A can zai yi jawabin shirin kafa sabuwar jam'iyarsa da ya ce za ta samarwa Amurka makoma kasancewar manyan shugab

Biden Ya Nemi Magoya Bayansa Su Tsaya A Gida Lokacin Rantsar Da Shi

A daidai lokacin da ake daf da rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden, an baza dubban jami'an tsaron soji domin murkushe duk wata zanga-zanga da ka iya barkewa. Tun a farkon makon da ya gabata ne dai Hukumar Leken Asiri ta Amurka ta FBI, ta yi gargadin cewa akwai yuwar samun tarzoma a ko'ina a kasar. Zababben shugaban dai ya shawarci jama'a da su yi zaman su a gida ba sai sun halarci bukin rantsarwar ba, ko baya ga matsalar annobar korona akwai yuwar dakarun sojin da aka baza na shirin maganin duk wanda ya nemi daukar dala ba gammo. Shugaba Donald Trump mai barin gado ya bayyana cewa zai bar babban birnin kasar Washington DC tun da sanyin safiyar gobe laraba, don kaucewa yin ido biyu da wanda zai gaje shi. A tarihin kasar dai wannan ne karon farko da za a yi bukin rantsarwa mafi tsaurin tsaro a Amurka, da kuma armashinsa ya ragu, muddin ta tabbata bai samu halarcin jama'a ba.

Akwai Yuwar Sake Rufe Makarantu A Nijeriya Saboda Korona

A irin yadda cutar korona ke ci gaba da kamari a duniya, mai yuwa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar na shirin bayar da shawara don sake kulle makarantu da zaran aka ga alkalumman masu kamuwa da ita na ci gaba da karuwa. An dai bude makarantun ne a ranar 18 ga wannan wata na Janairu, koda ya ke gwamnonin jahohin Kaduna da Edo ba su amince da bude makarantun ba. Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun gana da shuwagabannin kwamitin yaki da annobar korona don daukar mataki na gaba, da ake jin bai rasa alaka da sake rufe makarantun. Bayan bude makarantu a jiya, galibin al'ummar kasar sun yi suka akan matakin, da suka ce mai hadarin gaske ne saboda abu ne mai wuya hukumomin makarantu a Najeriya su iya cika ka'idojin da aka gindaya, kasancewar ajujuwa a makarantun makare suke da dalibai da zai yi wahala a bada tazara tsakani.

Wasu Daga Hotunan Gobarar Kasuwar Sokoto

DA DUMI DUMI Gobara Ta Kama A Babbar Kasuwar Sokoto

Tun da sanyin safiyar yau gobarar ta tashi a bangaren masu kayan robobi da ke Babbar Kasuwar Jahar Sokoto, abinda ya haddasa hasarar dukiyar da ba a kai ga gano adadinta ba a halin yanzu. Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin hanyar da motocin kashe gobara za su bi, wanda wannan ya kara hayyaka matsalar gobarar da ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan kasuwar. Wannan ya sa masu dukiyar da ke ci gaba da konewa rashin sanin madogara, face diban kayansu da hannuwa ko don tsira da wani abu. Wasu da TANTABARA ta samu zantawa da su, sun bayyana cewa su kam sun tafka hasara, domin karfin wutar ba zai bar su fitar da wasu muhimamman abubuwa ba. To sai dai babu wani rahoton jikkata ko rasa rai kawo yanzu, wanda shi ne abinda ake fata.

Da Dumi Dumi - An Tsige Shugaba Trump

Majalisar wakilan Amurka sun samu yawan kuri'un da za su kai ga tsige shugaba Donald Trump. Wannan ya tabbatar da shi a matsayin shugaban Amurka na farko da ka tsige har sau biyu. Kuma wannan zai hana ma sa sake rike kowane irin mukamin siyasar kasar nan gaba da kuma bada damar gurfanar da shi don fuskantar tuhuma a gaban kotu. Ga jerin shuwagabannin Amurka da aka taba tsigewa:  A shekarar 1868 an tsige shugaban Amurka Andrew Johnson,  Sai kuma shugaba Bill Clinton da aka taba tsigewa a 1998. Bayan sa kuma sai shugaban Amurka mai barin gado Donald J. Trump shi kuma  a 2019. Bayan nan kuma yau 13 ga watan Janairun 2021 an sake tsige tsohon shugaban a karo na biyu.

An Soma Jefa Kuri'ar Tsige Trump

'Yan majalisar wakilan Amurka yanzu haka sun soma jefa kuri'ar tsige shugaba Donald J. Trump. Sun soma kada kuri'ar ne bayan kammala muhawarar da ta bada damar ci gaba da daukar mataki na gaba, wanda shi ne kada kuri'ar amincewa ko akasin haka. An dai baza dubban jami'an tsaron soji a ko'ina ciki da harabar majalisar dokoki ta Capitol Hill don shirin ko ta kwana. Bayan kammala jefa kuri'ar daga baya za a turawa majalisar dattijai don daukan mataki na gaba da zai iya kai ga tsige shi ko sabanin haka. Idan har haka ta tabbata zai zama kenan Trump shi ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige har sau biyu. Wannan sabon matakin na da nasaba da jawaban shugaban a makon jiya, da 'yan majalisar suka ce sun kai ga tunzura magoya bayansa har suka kai wa majalisar hari da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, ciki kuwa har da jami'in dan sanda da ke kare masu zanga-zangar daga kutsa kai ginin majalisar.

Matsalar Tsaro Ta Addabi Jahar Sokoto

A daren jiya Talata ne wasu yan bindiga sukayi dirar mikiya a wani kauye mai suna Chacho da ke karamar hukumar mulki ta Wurno da ke jahar Sokoto. Rahotanni na cewa maharan sun kai wa wani Dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu samame ne da niyyar hallaka shi, amma da hakansu ba ta cimma ruwa ba suka yi awon gaba da mahaifinsa hadi da matarsa da kuma harbin kanensa, tare da karbar kudin da suke mallakarsa ne kimanin naira dubu dari shida da sittin. Maharan sun kuma harbe wani dan banga har lahira, mai suna Malam Rabi'u. Wannan lamarin yawitar hare-hare a jahar Sokoto na neman gagarar kundila, domin kwana daya kawai kafin wannan harin wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani gari da ke karamar hukumar ta Wurno da suka karbi kudi naira miliyan daya daga hannun wani dan kasuwa kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar kama biyar daga cikin su.

DA DUMI-DUMI 'Yan Majalisar Amurka Sun Soma Zama Don Tsige Trump

'Yan majalisar dokokin Amurka sun soma wani zama na musamman yanzu haka, don shirin tsige shugaba Donald Trump, ana sauran kwanaki 9 kacal a rantsar da zababben shugaban kasar Joe Biden. Kakakin majalisar dattawan kasar Nancy Pelosi a wata hira da tashar talabijin ta NBC, ta ce, "Mista Trump zai fuskanci zahiri ta hanyar girbar abinda ya shuka". Ta ce za su nemi mataimakinsa Mike Pence ya aminta tare da sa hannu akan kudurin dokar da zai nuna amincewa da cewa shugaba Trump bai dace ya shugabanci kasar ba, ko kuma idan har hakan ta ci tura, su soma jefa kuri'ar amincewa da tsige shi a tsakiyar makon nan. Idan har hakan ta tabbata wannan ya nuna Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taba tsigewa har sau biyu. Kuma hakan zai bata ma sa suna da makomar siyasa nan gaba. Masana shari'a na ganin bayan tsige shi, zai iya fuskantar tuhuma akan zargin ingiza magoya bayansa su kai hari da zanga-zanga a majalisar dokokin kasar, domin hana amincewa da zaben Joe