A irin yadda cutar korona ke ci gaba da kamari a duniya, mai yuwa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar na shirin bayar da shawara don sake kulle makarantu da zaran aka ga alkalumman masu kamuwa da ita na ci gaba da karuwa.
An dai bude makarantun ne a ranar 18 ga wannan wata na Janairu, koda ya ke gwamnonin jahohin Kaduna da Edo ba su amince da bude makarantun ba.
Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun gana da shuwagabannin kwamitin yaki da annobar korona don daukar mataki na gaba, da ake jin bai rasa alaka da sake rufe makarantun.
Bayan bude makarantu a jiya, galibin al'ummar kasar sun yi suka akan matakin, da suka ce mai hadarin gaske ne saboda abu ne mai wuya hukumomin makarantu a Najeriya su iya cika ka'idojin da aka gindaya, kasancewar ajujuwa a makarantun makare suke da dalibai da zai yi wahala a bada tazara tsakani.
Comments