Tun da sanyin safiyar yau gobarar ta tashi a bangaren masu kayan robobi da ke Babbar Kasuwar Jahar Sokoto, abinda ya haddasa hasarar dukiyar da ba a kai ga gano adadinta ba a halin yanzu.
Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin hanyar da motocin kashe gobara za su bi, wanda wannan ya kara hayyaka matsalar gobarar da ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan kasuwar.
Wannan ya sa masu dukiyar da ke ci gaba da konewa rashin sanin madogara, face diban kayansu da hannuwa ko don tsira da wani abu.
Wasu da TANTABARA ta samu zantawa da su, sun bayyana cewa su kam sun tafka hasara, domin karfin wutar ba zai bar su fitar da wasu muhimamman abubuwa ba.
Comments