Skip to main content

Posts

Showing posts from April 27, 2023

Me Ku Ka Sani Game Da Labari Maras DaÉ—i (Negative Story)?

Galibin wasu mutane na ganin 'yan jarida ba su cika bayar da labarai ma su daÉ—i ba face waÉ—anda suka shafi tashin hankali da tonon silili da Æ™wanÆ™wanto da kuma na haÉ—urra. Wannan fahimta kuwa na da nasaba da kasa fahimtar aikin jaridar kansa da wanda ke yin sa. Ni a ganina duk wani labari da ya shafi ayyukan muggan mutane da ya munanawa mutane na gari shi zan mayarwa hankali domin fallasa mai mugunta da farantawa wanda aka zalunta. Bari mu soma da mai sauÆ™i kafin mu duba ma su sarkakiya. Idan haÉ—ari ya faru, misali na mota ko jirgin sama ko na kasa ko kuma gobara ko ambaliyar ruwa; za mu bayar da labarin. Shin ka san ba muna bayar da labarin ne saboda kawai a ji an mutu ko an kaririye ko an yi hasarar dukiya ba? GA AMSA:  Game da haÉ—ari ko gobara da sauran iftila'i mu kan bayar da wannan labari saboda bayyana halin waÉ—anda matsalar ta rutsa da su, domin samun agajin hukumomi da masu iya tallafawa. Mu kan bayar da labarin saboda jawo hankalin hukumomin tsaro da saura