Skip to main content

Me Ku Ka Sani Game Da Labari Maras Daɗi (Negative Story)?

Galibin wasu mutane na ganin 'yan jarida ba su cika bayar da labarai ma su daɗi ba face waɗanda suka shafi tashin hankali da tonon silili da ƙwanƙwanto da kuma na haɗurra.
Wannan fahimta kuwa na da nasaba da kasa fahimtar aikin jaridar kansa da wanda ke yin sa.
Ni a ganina duk wani labari da ya shafi ayyukan muggan mutane da ya munanawa mutane na gari shi zan mayarwa hankali domin fallasa mai mugunta da farantawa wanda aka zalunta.
Bari mu soma da mai sauƙi kafin mu duba ma su sarkakiya.

Idan haɗari ya faru, misali na mota ko jirgin sama ko na kasa ko kuma gobara ko ambaliyar ruwa; za mu bayar da labarin.
Shin ka san ba muna bayar da labarin ne saboda kawai a ji an mutu ko an kaririye ko an yi hasarar dukiya ba?

GA AMSA: 

Game da haɗari ko gobara da sauran iftila'i mu kan bayar da wannan labari saboda bayyana halin waɗanda matsalar ta rutsa da su, domin samun agajin hukumomi da masu iya tallafawa. Mu kan bayar da labarin saboda jawo hankalin hukumomin tsaro da sauran jama'a su lura da musabbabin haɗarin idan na mota ne, ko jiragen ruwa (kamar kwale-kwale) da sauran su. Wannan zai sa a ji shin 'min indilLahi' ne ko kuwa an yi halin Ɗan Adam na ɗora kaya fiye da kima?
Kenan ba labarin ne kawai muke bayarwa kara-zube ba, muna da wani horo na musamman a ƙarƙashin bayar da labarin shi kansa.
Misali, a lokutan hunturu ya zama wajibi a yi nesa da duk wani makamashi irin asaha da ƙyastu da man fetur da ma kananzir, musamman ga yara. Baya ga faɗakarwa, hasalima akwai sanar da damuwar waɗanda lamarin ya shafa ga masu iya taimaka mu su.
Da ba mu bayar da labari irin na yaƙi da yunwa, da fari da kuwa Majalisar Ɗunkin Duniya har ma da hukumomin bayar da agaji ba su kai agajin gaggawa na kayan abinci da ruwan sha ga waɗannan jama'a ba. Da ba mu bayar da labari irin na ambaliyar ruwa da kifewar kwale-kwale da ɓarkewar annoba da curutoci irin na maleriya waɗanda hukumomin bayar da agaji irin NEMA da na NCDC, masu dakile cutuka masu yaɗuwa ba su san da shi ba to ina kuwa ga ɗaukar mataki!
2. A rukuni na biyu, matsayina na ɗan jarida, na kan saka ido game da lamurran da ke cikin jama'a da zamantakewarsu da muhalli da kewayensa da shuwagabannin talakawa na gargajiya da 'yan siyasa. 

Kullum rana kuwa zan nemi labarin tafiyar lamurra. An ɗora min alhakin zama ido da kunnuwan jama'a; in kuma zama bakinsu in da ba su iya magana. Kafin in ɗora alhakin zubar da shara barkatai kan gwamnati a lokaci guda, sai na lura su kansu mutane wace rawa suke takawa wajen tsaftace muhalli. Wato kenan idan Laila ta ƙi sai a koma Basha!
Idan annobar gudu da amai ta ɓarke a ƙauyuka da sassan birane, muddin zan haɗa rahoto, dole ne in saurari kowane ɓangare. Baya ga alhakin gwamnati na samar da magani, akwai kuma tsaftace ruwan sha. Baya ga kawo ma al'umma agaji, akwai kuma wayar mu su da kai na yadda za su lazimci tsaftar ruwa da kare kai. Wannan kenan sai na bi ta kan kowa: gwamnati, don sanin shin ta kai agaji da gaggawa, idan maleriya ce sun raba ragar sauro kan lokaci, ko suna bayar da magungunan da juddum hukumomin lafiya ke bayar da tallafi?
Su kuma jami'an kiyon lafiya na aikinsu wajen amfani da kafafen watsa kabari da taruka wajen wayar da kan jama'a tare da taimakon hukumomin lafiya ko kuwa su ma al'ummar gari. Sakamakon da zai fito shi ma zai zama abin misali ga wasu.

3. Rukuni na uku, shi ne na masu mulkin talakawa. Cikin su akwai masu yin ayyukan da talaka ya ɗora mu su, akwai kuma ma su watsi da wannan hakki. Idan gwamnati ta ƙaddamar da rabon kayan amfanin gona misali taki da garmar shanu da irin shuka da magungunan ƙwari ga manoma. Har ma aka gayyaci 'yan jarida domin su shaida.
Matsayina a nan shi in zama wakilin talaka, idonsa da kunnuwa da kuma bakinsa.
Shin mai karatu ka san irin labarin da nake nema a nan?
Idan ba ka sani ba to ga amsa:

A irin wannan yanayi, zan nemi labarin da zai amfani mai gaskiya tsakanin mahukunta da talakawansu. 

A irin wannan lamari, babban abin mayar da hankali shi ne:

1. Su wa aka zaɓa domin ba su tallafin, kuma saboda me aka zaɓe su?
2. Akwai waɗanda aka hanawa tallafin, kuma saboda me?

3. An saka siyasa a ciki?

4. A wane lokacin shekara aka bayar da tallafin (misali, farkon damina ne ko bayan an girbe amfanin gona, ko kuwa lokutan zaɓe ne?)

5. Sannan waɗanne irin jawabai gwamnati ta yi da za su sa in fahimci manufar bayar da tallafi.

6. Su waye suka nuna murna kuma su waye suka nuna rashin gamsuwa (misali, na su nuna damuwa 'yan adawa ne ko wake da shinkafa ne?)

To a nan ne fa wasu za su ce muna wallafa "negative stories" wato labaran da ba su da daɗi ga wasu mutane.

Zan mayar da hankalina ga ma su ƙorafi. In ji me ya sa su ke ƙorafin!
Su ne za su taimaka ma zaren labarina in bi shi tiryan-tiryan har sai na gano gaskiya. Zan yi amfani da muryoyinsu (idan sun amince da haka, idan kuma suna da shakku ga abinda zai faru da su, zan tabbatar da na ɓoye sirrinsu da kuma asalin inda na samo labarina).

Zan tunkari masu gari domin ji daga ɓangarensu. A wurin mahukunta wannan shi ne labari maras daɗin ji, musamman idan akwai badakalar cin hanci a cikin bayar da tallafin.
Zan nemi sanin dalilin ware wasu a bisa siyasa ko addini ko ƙabilanci. Zan nemi sanin dalilin da ya sa wasu suka yi ma gwamnati yarfe domin kawai adawar siyasa. Zan zama tsakiya da zimmar tabbatar da gaskiyar lamari, in fitar da kome a zahiri inda hakan zai kawar da zargi da kuma kare kaina.
Lallai ne duk labarin yabo da tallata wani ko wasu in guje shi domin ba shi ne aikina ba! Abinda nake nema shi ne, shin an yi ma talaka adalci ko an murkushe shi, ta haka zan san yadda zan fallasa badaƙalar.
To irin wannan ne wasu ke kira labari maras daɗin ji, negative story, wai daga an mutu sai an lalace.
ZUABIRU AHMAD BASHIR,ƊAN JARIDA NE A RADIYO NAJERIYA (FRCN).
MAI NEMAN TUNTUƁA TA:


Comments