Skip to main content

Biden Ya Doke Trump A Georgia Da Ratar Kuri'u 12,284

 An kammala kirga kuri'un jahar Georgia da ake takaddama kan ta, in da Joe Biden ya lashe jahar da rata mai yawa.

Jahar Atlanta Georgia mai yawan kuri'u miliyan biyar da doriya ta zama sha kallo a idon duniya ganin yadda shugaba Donald Trump ya yi zargin shi ne ya samu nasara a jahar kuma ya nemi sai an sake kirga dukan kurin'un da aka kada.

A jiya alhamis da yamma ne aka kammala lissafin da ya kwashe kusan fiye da mako daya a na yi, in da ofishin sakataren gwamnatin jahar ya fitar da wannan sanarwa.

Ofishin Brad Raffensperger ya bayyana cewa bayan sake kirga dukan kuri'un da hannu, sakamakon da aka samu tun farko yana nan bai sauya ba.

Joe Biden ya doke Donald Trump da yawan kuri'u 12,284, yayin da shugaba Donald Trump ya samu 1,872.

Comments