Skip to main content

Posts

Showing posts from March 10, 2022

Hukumar Hana Fasa Kwabri Ta Najeriya Ta Kama Buhunan Naman Jaki 1,339

Hukumar ta bayyana kama wannan adadin buhunan naman jaki ne a jahar Kabi da ke arewa maso yammacin Najeriya da aka kiyasta kudinsu ya haura naira miliyan 40. Shuguban hukumar ta kastam Joseph Attah ya ce sun yi nasarar kama kyafaffen naman jakin ne da aka shirya fita da shi. A cewar sa wadanda aka kama da naman sun bayyanawa hukumar cewa fiye da jakuna dubu daya suka yanka kafin su tara wannan adadi. Gwamnatin Najeriya dai ta haramta safarar jakuna zuwa kasashen ketare musamman kasar Sin, wadda ke sahun gaba wajen sayen jakuna a kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Mali da Sudan da sauran su. A halin da ake ciki yanzu haka jakuna na barazanar karewa a duniya sakamakon yawan safarar su da ake tare da sarrafa nama da fatarsu ta wasu hanyoyi na daban. Hasalima dai, jaki dabba ce da kan hai fi da daya kwal a cikin shekaru ba kamar sauran dabbobi ba da ke haihuwa biyu zuwa uku a shekara.