Skip to main content

Posts

Showing posts from November 21, 2020

Shin Kuna Da Labarin Al'ajubban Duniya 7

 Shin kun taba jin labarin abubuwan al'ajabi guda 7 da ake kira Seven Wonders of the World a turance? Idan ba ku taba ba to yau zamu fara kawo mu ku bayani game da su, inda zamu soma da Dalar Giza da ke kasar Misira. Ita dai wannan dala da kuke ganin hotonta a kasa, na da matukar ban mamaki; an gina ta ne dubban shekaru da suka gabata, tun a wajajen 2580 - 2560 kafin haihuwar annabi Isa. Tarihi ya nuna wani basaraken Misira mai suna Fir'auna Khufus ne ya gina ta, a matsayin babbar makabartar bizne manyan sarakunan Masar da aka fi sani da Fir'aunoni, da ma manyan tajiran wancan lokaci. Tsawonta ya kai mita 146.7 wato kafa 481 kenan. Haka ma fadin dalar Giza ya kai mita 230.34 ko kuma kafa 455 kenan. An yi amfani da birki ko bulo na manya manyan duwatsu da girmansu zai kai na mota marsandi, wanda miliyoyin bayi suka turo daga wurare masu nisan gaske zuwa inda aka gina dalar. Tarihi ya nuna an dauki tsawon shekaru 20 ana gina wannan dala kuma a halin yanzu tana da shekaru 3,80...

Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Da ASUU

 An kai matsaya tsakanin Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU in da gwamnatin tarayya ta amince da bukatunsu. A jiya jumu'a dai ne suka yi wani zama don ganin malaman sun janye yajin aikin da ya dauki watanni bakwai ana yi. A yanzu dai gwamntin Najeriya ta amince da cire malaman daga tsarin albashi na IPPIS wanda suka jima suna turjiya akai, kuma za ta biya malaman albashin duk watannin da su ke bi. Haka ma ministan kwadagon Najeriya Cris Ngige ya tabbatarwa manema labarai cewa, za a karawa malaman jami'ar alwus da zai kai naira biliyan 35 sabanin yadda yake a da na biliyan 30. Ngige ya kuma ce za a ci gaba da tattaunawa kan sabon tsarin albashi na UTAS muddin an kammala tsara shi. A nasu bangare kungiyar malaman jami'o'in sun yi maraba da wannan yunkuri, in da ake ganin matakin ga alama zai iya kawo karshen dogon yajin aikin da aka dade ana yi.