Shin kun taba jin labarin abubuwan al'ajabi guda 7 da ake kira Seven Wonders of the World a turance?
Idan ba ku taba ba to yau zamu fara kawo mu ku bayani game da su, inda zamu soma da Dalar Giza da ke kasar Misira.
Ita dai wannan dala da kuke ganin hotonta a kasa, na da matukar ban mamaki; an gina ta ne dubban shekaru da suka gabata, tun a wajajen 2580 - 2560 kafin haihuwar annabi Isa. Tarihi ya nuna wani basaraken Misira mai suna Fir'auna Khufus ne ya gina ta, a matsayin babbar makabartar bizne manyan sarakunan Masar da aka fi sani da Fir'aunoni, da ma manyan tajiran wancan lokaci.
Tarihi ya nuna an dauki tsawon shekaru 20 ana gina wannan dala kuma a halin yanzu tana da shekaru 3,800 da ginawa.
Cibiyar Raya Al'adu ta Duniya UNESCO ce ta kebe wajen a matsayin wurin tarihi da kuma ya zama daya daga abubuwan ban mamaki a duniya.
Comments