Skip to main content

Posts

Showing posts from December 17, 2020

Da Dumi Dumi - Daliban Makarantar Kimiyya Ta Kankara Sun Iso Gida

Yanzu yanzun nan daliban da aka sace a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kankara da ke jahar Katsina suka iso gida. Yaran su kimanin 340 cikin rakiyar jami'an tsaron soji da 'yan sanda, sun iso fuskokinsu cike da annuri, koda yake dukan su sun yi butu-butu da kura alamar wahala. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi waya da gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari in da ya taya shi murnar samun nasarar ceto yaran. An dai sace yaran a ranar jumu'a da dare da ta gabata a wata makarantar kwana da ke karamar hukumar Kankara a jahar ta Katsina. Gwamnatin jahar ba ta yi cikakken bayanin yadda aka karbo yaran ba, ko da ya ke a bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar da rana an ji wani mai garkuwa da yaran na fadin suna tattaunawa da gwamnati don karbar kudin fansa.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Kungiyar Boko Haram Ta Saki Bidiyon Yaran Da Aka Sace A Katsina

Kungiyar Boko Haram ta saki wani faifan bidiyo da ke nuna yaran nan daliban makarantar kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina, kwanaki biyar da sace su. A cikin bidiyon an ga wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar na magana cikin Hausa: "Don Allah ina rokon gwamnati da kada ta yi amfani da duk wasu 'yan sa kai, a rufe dukan makarantu. Kuma sojojin da ke tafe don taimakonmu don Allah su koma, ba za su iya yi wa (mayakan) kome ba". In ji yaron. A can bayan yaron an ga wasu yara kanana masu yawan gaske da ake umurta da su zauna, kuma da ba su fi shekara goma goma ba, suna kuka tare da rokon a taimaka a cece su daga hannun mayakan. Faifan bidiyon mai tsawon minti daya ya nuna yaran cikin kura da alamar gajiya a tattare da su, sakamakon tafiya mai nisa a kasa. Ana kuma jin muryar daya daga 'yan bindigar na gargadin gwamnati da kada ta dauki kowane matakin amfani da karfi. Yana mai jaddada cewa yaran na cikin koshin lafiya. A ranar jumu'ar da ta gabata ne maharan suka y...