Skip to main content

Posts

Showing posts from June 7, 2022

Yahaya Bello Ya Caccaki Buhari

Da ya ke jawabi a lokacin da ake gudanar da shirin zaben fitar da gwani, gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya nemi a zabe shi domin ya magance matsalar tsaro da karancin ilmi da ake fama da su yanzu haka a Najeriya. Ya ce, "akwai takaici ace wai yanzu malaman jami'a suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune a gida kuma an kasa magance wannan matsala mai saukin magancewa". Yahaya Bello wanda ya ce ba zai jaye ma kowa a neman tikitin shugaban kasa, ya kara da cewa shi matashi ne kuma matasa ya kamata a ba dama su mulki kasar nan ba tsofaffi da suka gaji ba. Ya yabawa shugaba Buhari akan saka hannu a kan dokar ba matasa damar tsayawa takara, in da ya ce abu ne mai kyau. Ya yi kira ga mata da sauran 'yan Najeriya da ya ce ana zalunta da su zabe shi. Dan takarar ya ce "yanzu haka babu tsaro ko kadan kuma an kyale, ana kashe mutane ana kona mu su dukiya kuma ana kallo an zura ido".

'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Fara Janye Ma Bola Tinubu

Kawo yanzu dai akwai masu neman mukamin shugaban kasa da suka fito kafin fara jefa kuri'a suka bayyana cewa sun janye takararsu kuma sun marawa tsohon gwamnan jahar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Daga cikin su akwai gwamnan jahar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar da Fayemi Kayode da Ajayi Boroffice da tsohon kakakin majilasar wakilai Dimeji Bokole da kuma Gidein Akpabio. Amma Pasto Tunde Bakari ya bayyana cewa shi kam ba zai jaye ma kowa da ga cikin 'yan takara ba, kasancewar "ba su da kyakkyawar manufar gina kasa face rusa ta", in ji shi. Akwai 'yan takara da dama da ya zu haka su ke jiran a fara kada kuri'a da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Ahmed Yariman Bakura da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rotimi Amechi da sauran su. Zamu kawo mu ku karin labari nan gaba.