Skip to main content

Yahaya Bello Ya Caccaki Buhari

Da ya ke jawabi a lokacin da ake gudanar da shirin zaben fitar da gwani, gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya nemi a zabe shi domin ya magance matsalar tsaro da karancin ilmi da ake fama da su yanzu haka a Najeriya.
Ya ce, "akwai takaici ace wai yanzu malaman jami'a suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune a gida kuma an kasa magance wannan matsala mai saukin magancewa".

Yahaya Bello wanda ya ce ba zai jaye ma kowa a neman tikitin shugaban kasa, ya kara da cewa shi matashi ne kuma matasa ya kamata a ba dama su mulki kasar nan ba tsofaffi da suka gaji ba.
Ya yabawa shugaba Buhari akan saka hannu a kan dokar ba matasa damar tsayawa takara, in da ya ce abu ne mai kyau.

Ya yi kira ga mata da sauran 'yan Najeriya da ya ce ana zalunta da su zabe shi. Dan takarar ya ce "yanzu haka babu tsaro ko kadan kuma an kyale, ana kashe mutane ana kona mu su dukiya kuma ana kallo an zura ido".


Comments