Skip to main content

Ba Mu Yarda Da Sulhu Ba - Tambuwal

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi watsi da sakamakon taron da aka yi na amincewa da mutum daya da zai tsaya takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a 2023.

Gwamna Tambuwal ya yi watsi da hakan ne ta hannun daya daga cikin kungiyoyin yakin neman zabensa, Tambuwal Campaign Organisation (TCO).
A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Daraktanta, Nicholas Msheliza a ranar Juma’a ta ce
“Ofishin Kamfen din Tambuwal (TCO) ya ja kunnen wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar da za zabi daya a matsayin maslaha daga cikin mu hudu, kuma wannan karya ce tsagwaronta sannan ba daidai ba ne

“Gaskiyar lamarin ita ce kungiyar ta hadu a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, inda suka yi taron bita;  kuma, gaba É—aya sun yarda cewa tsarin yarjejeniya ba ya aiki.

“Tawagar ta kuma amince da cewa Sanata Saraki ya fito da daftarin bayani kan yadda zai isar da wannan shawara ga al’ummar Najeriya.  Wannan shine karo na Æ™arshe da membobin Æ™ungiyar suka zauna kuma suka amince da juna akan komai. Taron da ake shirin yi na nazari da tantance bayanan da aka shirya gudanarwa da misalin karfe 10 na rana, Sanata Saraki ne ya soke shi ta hanyar sakon WhatsApp", in ji bangaren na gwamna Tambuwal.

“Duk da haka, a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, 2022, Sanata Saraki ya sake yada wani sakon WhatsApp da ke nuna cewa ‘yan kungiyar su nufi Minna domin yin taro a ranar Juma’a, Gwamna Tambuwal ya sanar da sauran ‘yan kungiyar cewa, ba fa za a yi sulhu ba, kuma ba shi da hannu a duk wani abu mai kama da haka".  
Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Tambuwal bai halarci taron na ranarJuma'a a Minna ba.  A cewar sanarwar wannan na da nasaba da rashin tasirinsa kasancewar shirin samar da dan takara daya ta hanyar sulhu ya ruguje.

Tantabara News ta samu labarin cewa domin kaucewa shakku, Gwamna Tambuwal ya mika fom din takararsa na shugaban kasa, kuma a yanzu da neman dan takarar da bai dace ba daga cikin hudun ya ruguje, zai ci gaba da fuskantar tantancewa da kuma tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP.
Gwamna Tambuwal dai, ya sha fafutukar ganin an cimma matsaya a tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP daga yankin Arewa domin su fito da dan takarar da suka amince da shi ya tsaya takarar yankin a zaben fidda gwani da zai gudana a watan Mayun gobe.

Comments