Skip to main content

Posts

Showing posts from July 10, 2021

Littafan Da Abduljabbari Ya Nemi Ya Karanto A Wurin Mukabalar Da Ta Gabata

Abduljabbari Ya Kasa Kare Kansa

Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami'ar Bayaro da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace baya ga kame-kame da Abduljabbar ke yi babu wata tambaya daya tak da ya amsa. Ya kara da cewa a maimakon ya bude wagagen littafan nan da ya zo da su don fiddo da hujja sai kawai ya ce babu lokaci. A kan hala ya yanke hukuncin cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya kasa kare kansa. A na sa bangare Abduljabbar ya nemi a dai sake ba shi wani lokaci, watakila idan ya shirya, kuma ga hujja, zai iya tuba. Sai dai Malam Abubakar Madatai, daya daga masu gudanar da muhawarar, ya roki a sake ba Abduljabbar karin lokacin ya ke ta bukata. Su sun shirya amma ya ce shi bai shirya ba don haka a ba shi karin lokacin, kazalika ya nemi gwamnatin jahar Kano da nan gaba idan an amince da bukatar to a bada damar watsawa a gidajen rediyo da talabijin kowa ya ji ya gani.

Abduljabbari Ya Ce Idan An Ba Shi Sarari Zai Tuba

 Abduljabbari ya koka a kan yadda mukabalar ke tafiya, duk da ya kasa amsa muhimman tambayoyin da aka yi masa. Ya ce mintina 10 da aka ba shi don ya amsa tambayoyin da suka shafi cin zarafin Annabi (s.a.w.) ba za su isa ya kwance littafai kusan 500 da ya zo da su ba. An tambai shi ko a wane hadisi aka kira annabi bunsuru ko arne? Ya ce idan an ba shi karin lokaci zai binciko hadisan ya zo da su amma yanzu an kure shi ba cikin shiri yake ba, kuma gaba daya a cewar sa, babu gaskiya a mukabalar. Ya ce yana son ne ya tsamo mutane daga halakar da ke sa suna yin ridda sakamako rudanin hadisan. Kasancewar wannan kasawa ya sa daya daga Malaman da ke zurara masa tambayoyi Malam Abubakar Madatai ya neme shi da ya tuba ya tabbatar da kuskuren da ya yi. Amma Abduljabbar ya ce ta ya zai tuba a wajen wannan muÆ™abala, a gaban kowa da kowa, ba tare da ba shi karin lokaci don haduwa ta gaba ba, sannan a ba shi karin wasu hujjoji da suka fi nasa.  Da ya ki tuba, malamin na bangar