Skip to main content

Abduljabbari Ya Kasa Kare Kansa

Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami'ar Bayaro da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace baya ga kame-kame da Abduljabbar ke yi babu wata tambaya daya tak da ya amsa.
Ya kara da cewa a maimakon ya bude wagagen littafan nan da ya zo da su don fiddo da hujja sai kawai ya ce babu lokaci. A kan hala ya yanke hukuncin cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya kasa kare kansa.
A na sa bangare Abduljabbar ya nemi a dai sake ba shi wani lokaci, watakila idan ya shirya, kuma ga hujja, zai iya tuba.
Sai dai Malam Abubakar Madatai, daya daga masu gudanar da muhawarar, ya roki a sake ba Abduljabbar karin lokacin ya ke ta bukata. Su sun shirya amma ya ce shi bai shirya ba don haka a ba shi karin lokacin, kazalika ya nemi gwamnatin jahar Kano da nan gaba idan an amince da bukatar to a bada damar watsawa a gidajen rediyo da talabijin kowa ya ji ya gani.

Comments