A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙ ara ta’azzara a jahar Sokoto, kwamishinan tsaron jahar Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya bayar da sanarwar aje mu ƙ aminsa tare da ficewa daga jam’iyyar jam’iyar PDP mai mulkin jahar. A cewar tsohon kwamishinan tsaron, “akwai gaggan matsaloli da suka taka rawa wajen ficewarsa daga jam’iyayar, da suka ha ɗ a da sakacin gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal na watsi da dukan shawarwarin da ake ba shi da suka shafi tsaro; kazalika da rashin sauraren ƙ orafe- ƙ orafen dangane da ci gaban jahar a fannoni da dama”. A ranar alhamis da ta gabata dai wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a garin Chakai da ke Ƙ aramar Hukumar Mulki ta Tambuwal, wadda ita ce mahaifar gwamnan jahar, in da suka sace mutum goma sha bakwai ciki har da mata da ƙ ananan yara, tare da neman diyyar naira miliyan takwas da dubu ɗ ari biyar. Kazalika, sun fitar da sanarwar shirin hallaka mutanen daga gobe talata, muddin ‘yan uwan wadanda ake garkuwa da sun ba su aika...