Skip to main content

Posts

Showing posts from April 15, 2023

Halin Da Ake Ciki Kan Yunƙurin Juyin Mulki A Sudan

Jami'an Ɗaukin Gaggawa don Tallafa ma Tsaro a Sudan na Rapid Support Forces (RSF) a yau asabar sun ce sun ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa da gidan hafsan hafsoshin soji da babban filin jirgin sauka da tashin jiragen sama a birnin Khartoum a wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a lokacin da rikici ya ɓarke tsananinsu da sojoji. Rundunar ta RSF wacce ta zargi sojojin da fara kai mata hari, ta kuma ce sun ƙwace tashoshin jiragen sama a arewacin garin Merowe da kuma El-Obeid a yammacin ƙasar. Rundunar sojin saman Sudan na ci gaba da fatattakar mayaƙan RSF, a cewar wata sanarwa rundunar.   Wasu gidajen talabijin sun nuna wani jirgin soji a sararin samaniyar birnin Khartoum, amma Tantabara News ba ta tabbatar da sahihancin labarin. Rahotanni da ke shigo muna yanzu haka na bayyana cewa ana iya jin ƙarar harbe-harbe a sassa da dama na birnin Khartoum inda wasu shaidun gani da ido da ke bayar da rahoton harbe-harbe a garuruwan da ke makwabtaka da su, lamarin da ya sa ake fa...

Iran Ta Sha Alwashin Murƙushe Masu Tallata Manufar Cire Hijabi

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilun da ya gabata ne mataimakin babban lauyan ƙasar Iran ya bayyana cewa, za a gurfanar da mutanen da ke ƙarfafa mata gwiwar cire hijabi a gaban kotunan laifuka, kuma ba za su sami damar daukaka ƙara kan duk wani hukunci da aka yanke musu ba. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar mata da ke bijirewa dokokin sanya hijabi da Iran ta sanya, inda suke bayyana a manyan kantuna da gidajen cin abinci da shaguna da sauran wuraren taruwar jama'a.  A cikin 'yan watannin nan wasu mata masu fafutuka sun fito fili sun yaɗa hotunan kansu a shafukan sada zumunta ba tare da lullubi ba. Jami'an tsaron 'yan sandan Iran a ranar Asabar ɗin makon jiya, sun sanya na'urorin ɗaukar hoto a wuraren taruwar jama'a don tantancewa da kuma hukunta matan da aka gano ba su sanye da hijabi, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Iran suka ruwaito.   Kamfanin dillancin kabaran Reuters ya ruwaito mataimakin babban lauyan gwamnatin ƙa...

Wanene Ɗan Jarida?

Ɗan jarida mutum ne kamar kowa, sai dai tunaninsa da manufofinsa kan tafi daidai ne kawai da ra'ayin MASU SAURARO ta fuskokin da suka shafi aikinsa. Ya zama mai wakiltar waɗanda ba su da baki ne ko kafafuwan zuwa, kuma idanuwan talakawa a kowane lokaci. Idan ka nuna ma sa launi shuɗi, ƙoƙarin ya ke ya tabbatar da launin nan shuɗi ne ziryan ko yana da garwaye? Idan ka ce ma sa labarin abu kaza ya faru, ba zai ce a'a ba kuma ba zai ce eh ba, aikinsa shi ne TABBATARWA . Idan mai sauraro namiji ne ko mace ko mai ra'ayin wani addini ko akida ko mai kuɗi ko talaka, ɗan jarida kan GIRMAMA kowa, kuma zai ɗauki kowa a matsayin DAIDAI ta fuskar ba su damar bayyana ra'ayoyinsu. Ɗan jarida kan tafi da zamani, ya kuma rungumi fasahar da ƘIRƘIRA ta kawo domin tafiya daidai lokaci. A kowace marra GASKIYA ita ce madogarar ɗan jarida, kuma wannan kan ƙara sa masu sauraro su amince da shi. Amma kuma, dole ne ɗan jarida ya zama MAI IKON KANSA , ba zai yi ma kowa alfarma b...