Skip to main content

Wanene Ɗan Jarida?

Ɗan jarida mutum ne kamar kowa, sai dai tunaninsa da manufofinsa kan tafi daidai ne kawai da ra'ayin MASU SAURARO ta fuskokin da suka shafi aikinsa. Ya zama mai wakiltar waɗanda ba su da baki ne ko kafafuwan zuwa, kuma idanuwan talakawa a kowane lokaci.
Idan ka nuna ma sa launi shuɗi, ƙoƙarin ya ke ya tabbatar da launin nan shuɗi ne ziryan ko yana da garwaye?

Idan ka ce ma sa labarin abu kaza ya faru, ba zai ce a'a ba kuma ba zai ce eh ba, aikinsa shi ne TABBATARWA.

Idan mai sauraro namiji ne ko mace ko mai ra'ayin wani addini ko akida ko mai kuɗi ko talaka, ɗan jarida kan GIRMAMA kowa, kuma zai ɗauki kowa a matsayin DAIDAI ta fuskar ba su damar bayyana ra'ayoyinsu.

Ɗan jarida kan tafi da zamani, ya kuma rungumi fasahar da ƘIRƘIRA ta kawo domin tafiya daidai lokaci.

A kowace marra GASKIYA ita ce madogarar ɗan jarida, kuma wannan kan ƙara sa masu sauraro su amince da shi.

Amma kuma, dole ne ɗan jarida ya zama MAI IKON KANSA, ba zai yi ma kowa alfarma ba, ba zai bi ra'ayin wani gungun jama'a ba, ko sauraren barazanar wani ko wasu ba, face ra'ayin kafar da ya ke yi ma aiki da kuma ya zo daidai da na jama'a.

Ya zama mai BIN DIDDIGI, ya fallasa masu almubazzaranci da dukiyar talaka, ya hana ɓarnata kuɗi tamkar dai nasa ne. Mu wakilan talakawa ne, mun zama idanuwansu da bakunansu, ba zamu yi nadamar faɗar gaskiya ba.

Zubairu Ahmad Bashir (Kasarawa)
Ɗan Jarida ne a Rediyon Tarayyar Nigeria (FRCN)

Comments

Unknown said…
Allah ya kara bada ikon dadin gaskiya kome dacinta

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey