Skip to main content

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidajen Ma'aikatan Filayen Jiragen Saman Najeria Tare Da Sace Mutum 11


Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidajen ma'aikatan Hukumar Filin Jirgin Saman Tarayyar Najeriya da ke Kaduna, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 11.
Rahotannin baya-bayan nan sun kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi nasarar sace ma’aikacin Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA)A, da matarsa, da jami’in Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) da ya’yansa, kuma har yanzu ba a san inda suke ba.
Satar mutane ya zama ruwan dare a Najeriya a yau, kuma kusan kowace safiya ana samun rahotannin kashe-kashe ko satar mutane don neman kudin fansa. 
A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen satar mutane a Najeriya amma ga dukkan alamu kalaman nasa ba su yi tasiri ba.





Comments