Skip to main content

Posts

Showing posts from March 11, 2022

Karancin Man Fetur Ya Mayar Da Tituna Fayau

Yau an wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai na jahar Sokoto sakamakon tsananin karancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya fiye da wata biyu. Galibin hanyoyin mota sun zama kusan fayau sabanin yadda aka saba, yayinda dimbin direbobi suka mamaye ciki da harabar gidajen man jahar.  Tantabara News ta samu zantawa da wasu da ke kokarin samun man da suka bayyana cewa abin ya wuce hankali. Wani direba mai suna Umar Dogon Daji ya ce, " a watannin baya muna sayen litar mai naira 165, amma yanzu akwai in da ya kai har 260". Duk da irin wannan yanayi babu wata alamar kawo karshen wannan matsala da ta addabi kasar nan tsawon shekaru. Wani dan bunmburutu ya sanar da wakilinmu irin yadda su ma suke shan wahala kafin su samu nasarar sayen mai a kasuwar bayan fage. Mutumin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, " mu ma 'yan bunmburutu muna shan wuya kwarai da gaske, sai ma mun bayar da toshiyar baki sannan a ke zuba muna man". Ya kara