Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi watsi da sakamakon taron da aka yi na amincewa da mutum daya da zai tsaya takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a 2023. Gwamna Tambuwal ya yi watsi da hakan ne ta hannun daya daga cikin kungiyoyin yakin neman zabensa, Tambuwal Campaign Organisation (TCO). A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Daraktanta, Nicholas Msheliza a ranar Juma’a ta ce “Ofishin Kamfen din Tambuwal (TCO) ya ja kunnen wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar da za zabi daya a matsayin maslaha daga cikin mu hudu, kuma wannan karya ce tsagwaronta sannan ba daidai ba ne “Gaskiyar lamarin ita ce kungiyar ta hadu a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, inda suka yi taron bita; kuma, gaba É—aya sun yarda cewa tsarin yarjejeniya ba ya a...