Skip to main content

Posts

Showing posts from December 1, 2020

Kungiyar Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kisan Manoma 78 A Jahar Borno

A cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a yau, shugabanta Abubakar Shikau ya ce su ne suka aikata kisan manoman a garin Zabarbarin jahar Borno. Shikau ya ce sun yi wannan ne saboda fansa game da abinda sojojin Najeriya ke yi musu da taimakon al'umma. In da ya ci gaba da cewa da dama daga mazauna yankunan na tseguntawa jami'an tsaro maboyarsu, wanda hakan kan kai ga kama su. Shugaban kungiyar ya ce, sun dauki matakin yanka duk wanda ya ci gaba da tseguntawa jami'an sojoji sirrinsu. Har kawo yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wannan sabuwar sanarwa da kungiyar Boko Haram ta fitar ba.

Gwamnatin Tambuwal Na Shirin Ba Da Mamaki

Gwamnatin jahar Sokoto ta yunkoro wajen samar da ayukkan raya gari, tun daga soma aikin Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Jahar Sokoto da kuma Makarantar 'Yan Mata da ke garin Kasarawa galibin mazauna jahar ke ganin cewa an soma samun sauyi. Ganin yadda aka soma wasu ayukan da aka yi shekaru ana jira. Kuma cikin sauri da kamala. Tun lokacin zuwan gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal a 2015, galibin jama'a ke fadin albarkacin baki ganin gudanar da ayukkan kamar da wasa. To sai dai kuma, gwamnatin ta bayar da kwangiloli da suka hada da gina gadojin sama guda biyu da aka ce za a gina nan take. Kazalika da samar da filin wasa katafare da aka ambata da sauran su. TANTABARA ta zanta da wasu mazauna yankunan da ake ayukan in da suka shaida mata cewa suna murna da samar da ci gaban idan har ya tabbata. Haka ma wasu da dama sun soma samun hanyar abin kaiwa bakin salati daga soma ayukkan, inda suka kakkafa sana'o'insu a wuraren. A ziyarar da TANTABARA ta kai wura

'Yan Majalisa Sun Nemi Buhari Ya Yi Garambawul Ga Manyan Jami'an Sojoji

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake lale akan sha'anin tsaro. 'Yan majalisar dai sun nemi Buhari ya yiwa manyan hafsoshin sojin kasar garambawul, tare da sanya sabbin jini.  Sanata Kashim Shatima ya bayyana damuwarsa tare da shawartar shugaban kasa da ya sa a yi bincike kan lamarin tare da tabbatar da an magance matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas. Shatima ya ce "wannan lamari ne da ya zama wajibi a dauki tsattsauran mataki game da shi". Shi ma sanata Adamu Aleiro daga jahar Kabi, a wani sako da ya aike a rubuce, ya bayyana cewa, "bai kamata shugaba Buhari ya aike da tawaga a jahar Borno don yin jaje ba, da kan sa ya dace ya je". Aleiro ya kuma shawarci shugaba Buhari da yayi garambawul ga manyan jami'an sojoji Najeriya tare da maye su da sabbin jini. Rikicin Boko Haram dai ya kwashe shekaru 11 yana addabar yankin arewa maso gabascin Najeriya, kuma yayi sanadiyyar hallakar dubban rayuka