Skip to main content

Kungiyar Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kisan Manoma 78 A Jahar Borno

A cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a yau, shugabanta Abubakar Shikau ya ce su ne suka aikata kisan manoman a garin Zabarbarin jahar Borno.

Shikau ya ce sun yi wannan ne saboda fansa game da abinda sojojin Najeriya ke yi musu da taimakon al'umma. In da ya ci gaba da cewa da dama daga mazauna yankunan na tseguntawa jami'an tsaro maboyarsu, wanda hakan kan kai ga kama su.
Shugaban kungiyar ya ce, sun dauki matakin yanka duk wanda ya ci gaba da tseguntawa jami'an sojoji sirrinsu.
Har kawo yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wannan sabuwar sanarwa da kungiyar Boko Haram ta fitar ba.

Comments