Skip to main content

'Yan Majalisa Sun Nemi Buhari Ya Yi Garambawul Ga Manyan Jami'an Sojoji

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake lale akan sha'anin tsaro. 'Yan majalisar dai sun nemi Buhari ya yiwa manyan hafsoshin sojin kasar garambawul, tare da sanya sabbin jini. 
Sanata Kashim Shatima ya bayyana damuwarsa tare da shawartar shugaban kasa da ya sa a yi bincike kan lamarin tare da tabbatar da an magance matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas. Shatima ya ce "wannan lamari ne da ya zama wajibi a dauki tsattsauran mataki game da shi".
Shi ma sanata Adamu Aleiro daga jahar Kabi, a wani sako da ya aike a rubuce, ya bayyana cewa, "bai kamata shugaba Buhari ya aike da tawaga a jahar Borno don yin jaje ba, da kan sa ya dace ya je".
Aleiro ya kuma shawarci shugaba Buhari da yayi garambawul ga manyan jami'an sojoji Najeriya tare da maye su da sabbin jini.
Rikicin Boko Haram dai ya kwashe shekaru 11 yana addabar yankin arewa maso gabascin Najeriya, kuma yayi sanadiyyar hallakar dubban rayuka gami da hasarar dukiya.
A 'yan shekarun nan dai matsalar tsaro ta addabi yankunan arewacin Najeriya, wanda baya ga ayukan 'yan ta'adan Boko Haram da kungiyar mayan IS, shiyar arewa maso yamma na fuskantar matsalar 'yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, a jahohin Zamafara da Sokoto da Katsina da sauran su.
Idan ana iya tunawa dai, ranar jumu'ar da ta gabata ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe a kalla manoman shinkafa 43 a kauyen Zabarmari na jahar Borno.

Comments