Skip to main content

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa. 
Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace.

Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Comments