Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya umurci Malaman Jamiāar Jahar Sokoto da su koma bakin aiki ba da bata lokaci ba,bayan kwashe wata shida jamiāar na rufe sakamakon yajin aikin Kungiyar Malamn Jamiāa (ASUU). Wannan mataki na kama da bayar da umurnin nan take in da ya nuna matukar bacin ransa yadda malaman ke ci gaba da kauracewa wuraren aikinsu da zimmar bin umurnin kungiyar ta ASUU. Ya kuma nunar da cewa babu wani hakki da malaman jamiāar Jahar Sokoto ke bin gwamnatinsa kama daga albashi ya zuwa sauran bukatu da bai yi mu su ba. Ya bayyana cewa babu wata matsala a duniya da ta gagari tattaunawar da za ta kai ga cimma maslaha, kuma ya zama wajibi a fito da matakin da zai iya zama kandagarki ga duk wani abu da ke haifar da yajin aiki a Najeriya. āBai kamata ku biyewa uwar kungiya ta ASUU ba, saboda matsalolinsu ba su shafe ku ba. Kuna cutar da dalibanku ne kawai, kuma wannan biyayyar da kuke ci gaba da yi na da matukar muni da nakasu ga makomar i...