Skip to main content

Posts

Showing posts from March 18, 2022

Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya

Bayan shafe 'yan kwanaki a birnin Landan na Burtaniya in da aka duba lafiyarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya a sauka Abuja yau da dare.

Malami Ya Ce Zai Bi Umurnin Kotu Ya Goge Sashe na 84 (12)

Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya ce cikin gaggawa zai bi umurnin wata babbar kotun Najeriya da ta bukaci a goge sashe na 84 da ya tilasta duk masu rike mukaman siyasa aje mukamansu kwana 30 kafin zabe. KUNA IYA KARANTA: http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/babbar-kotun-tarayya-ta-bayar-da.html Malami dai ya tabbatar da cewa, zai yi ma dokar gyaran fuska. Tun da farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hannu tare da rokon 'yan majalisar dattawan Najeriya da su yi ma ta kwaskwarima wajen cire wannan sashe, amma suka ki amincewa da wannan bukata. Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan kafin gudanar da babban zaben jam'iyyar APC da zai gudana a ranar 26 ga wannan wata na Maris. Kuma a na ganin zai iya kara haifar da baraka cikin jam'iyyar.

Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Da Umurnin Soke Sashe na 84 Da Ya Hana Masu Rike Da Mukaman Siyasa Tsayawa Takara

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Umuahia, Jihar Abia, ta umurci Babban Lauyan Tarayya da ya gaggauta soke sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.  Yayin da yake rattaba hannu a kan kudirin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta soke sashe na 84 (12), wanda ya haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba. Shugaban ya kara da cewa, “Sashe na 84 (12) ya kunshi hana masu rike da mukaman siyasa damar kada kuri’a ko zabe a babban taro ko na kowace jam’iyya, domin gabatar da ‘yan takara a kowane zabe.  Sai dai Majalisar Dattawa ta ki yin la’akari da bukatar shugaban kasar, inda ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman a yi wa sashen kwaskwarima, inda ‘yan majalisar suka jaddada cewa gyaran sashe na 84 (12) zai saba wa ma’aikatan gwamnati.  

Illolin Amfani Da Rikitacciyar Jimla A Rubutu Ko Rediyo

Papertrue.blog *" A kokarin hada su da 'yan'uwansu da sanadiyyar rikice-rikice suka rabu ." A yadda harshe ya ke da wuyar sha'ani wajen aikewa da sako, wajibi ne a kaucewa kowace irin jimla mai harshen damo ko mai iya haddasa rudani a kwalkwalwar mai karatu ko saurare. A maimakon haka ya fi dacewa a ce, " A kokarin hada su da 'yan'uwansu da tashe-tashen hankula suka raba" Dalili kuwa kalamar rikici ba ta dace da nan ba saboda ko mutum biyu na iya rikici da juna.  Rikici na nufin jayayya ko rashin yarda da abu da zai iya haifar da rashin matsaya daya, wanda kuma zai kai ga fada. Mutane na iya yin gaba da juna akan rikici na siyasa ko gado. Amma ita kalmar tashin hankali a bayyane ta ke ga mai saurare, sakamakon irin yadda kalmar ta zama tamkar ta yi kaka-gida saboda yadda yankunan arewacin Najeriya ke fama da tashe-tashen hankula. Me Ya Kawo Rudani A Nan? A jimla ta farko mai saurare zai dauka rikicin tsakanin 'yan'uwan ya ke,

Bambancin Bayar Da Labari A Rediyo Da Kuma Talabijin

Shi mai gabatar da shiri a rediyo kullum ya sani sauraren sa ake yi, ba kamar yadda ake kallo a talabijin ba, kan haka dole ya yi amfani da  descriptive words, wato kalmomi masu hoto ,  domin mai saurare ya ga hoton abin a kwakwalwarsa, har ma ya ji dadi a ransa. Getty images Ya Misalin Haka Ya Ke Ga Mai Saurare? Mai saurare na bukatar ganin zahirin hoton abinda mai bayar da labari ke fada. Kunnuwa ke sauraren labarin amma kwakwalwa za ta ci gaba da sarrafa hoton abinda ake siffatantawa. Misalain haka shi ne a suranta maka gida ta hanyar zayyano dukan abinda ya mallaka, kamar kofofi biyu hannun riga da juna da farin fenti sai tagogin gilashi ma su karau-karau ga kuma furanni da aka kawata harabarsa farare da jajaye da kuma rawaya. Nan ta ke kwakwalwar mai saurare za ta dauki hoton har yadda za ku iya ganin sa. Ga Misalin Haka: "Gaba daya kankara ta mamaye tsaunukan sun yi fari fat tamkar auduga. A duk shekara irin wannan lokcin sanyi, ruwan gulabe da rafukk

Ranar Bacci Ta Duniya Ta Zagayo

Kowace rana ta Allah na da nata amfani: aiki da karatu da ibada. Majalisar Dunkin Duniya ta kebe kowace rana kamar yadda yau ta zama ranar bacci ta duniya. Shin ko kun san bacci na kara lafiyar kwakwalwa da taimaka ma mai karatu, kuma wadanne lokuta kuka fi jin dadin bacci?