Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya ce cikin gaggawa zai bi umurnin wata babbar kotun Najeriya da ta bukaci a goge sashe na 84 da ya tilasta duk masu rike mukaman siyasa aje mukamansu kwana 30 kafin zabe.
KUNA IYA KARANTA:
Malami dai ya tabbatar da cewa, zai yi ma dokar gyaran fuska. Tun da farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hannu tare da rokon 'yan majalisar dattawan Najeriya da su yi ma ta kwaskwarima wajen cire wannan sashe, amma suka ki amincewa da wannan bukata.
Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan kafin gudanar da babban zaben jam'iyyar APC da zai gudana a ranar 26 ga wannan wata na Maris. Kuma a na ganin zai iya kara haifar da baraka cikin jam'iyyar.
Comments