Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Da Umurnin Soke Sashe na 84 Da Ya Hana Masu Rike Da Mukaman Siyasa Tsayawa Takara
Yayin da yake rattaba hannu a kan kudirin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta soke sashe na 84 (12), wanda ya haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba. Shugaban ya kara da cewa, “Sashe na 84 (12) ya kunshi hana masu rike da mukaman siyasa damar kada kuri’a ko zabe a babban taro ko na kowace jam’iyya, domin gabatar da ‘yan takara a kowane zabe.
Sai dai Majalisar Dattawa ta ki yin la’akari da bukatar shugaban kasar, inda ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman a yi wa sashen kwaskwarima, inda ‘yan majalisar suka jaddada cewa gyaran sashe na 84 (12) zai saba wa ma’aikatan gwamnati.
Comments